DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, September 15, 2026
HomeBabban Labari Jihohi 31 na Nijeriya sun ɓatar da Naira biliyan 252 a fannin...

Jihohi 31 na Nijeriya sun ɓatar da Naira biliyan 252 a fannin tsaro cikin watanni shida – Bincike

Jihohi 31 na Nijeriya sun ɓatar da Naira biliyan 252 a fannin tsaro cikin watanni shida – Bincike

Akalla gwamnatocin jihohi 31 a Najeriya sun ɓatar da kimanin Naira biliyan 252.26 wajen yaki da aikata laifuka da dakile matsalar rashin tsaro a cikin watanni shida na farkon shekarar 2026.

Jaridar Punch ta ruwaito binciken bayanan kasafin kudin jihohi na rubu’i na farko zuwa na biyu na shekarar 2026, wanda aka samu daga Open Nigerian States, ya nuna cewa jihar Kogi ce ta fi kowace jiha narka kudi wajen tsaro, inda ta sanya Naira biliyan 34.67, wato kashi 13.74 na jimillar kudin da aka ɓatar.

Plateau ce ta biyo baya da Naira biliyan 23.69, yayin da Bauchi ta zo ta uku da Naira biliyan 22.35.

Jihohin uku kadai sun kashe kusan Naira biliyan 80.70, wanda ya kai kashi 32 cikin 100 na jimillar kudaden tsaron da aka tattara a cikin bayanan.

Sauran jihohin da aka samu bayanan kashe kudaden tsaro sun hada da Abia, Adamawa, Anambra, Bayelsa, Benue, Borno, Cross River, Delta, Ebonyi, Ekiti, Enugu, Gombe, Imo, Jigawa, Kaduna, Kano, Katsina, Kebbi, Kwara, Lagos, Nasarawa, Niger, Ogun, Ondo, Oyo, Sokoto, Taraba da Zamfara.

Kudaden sun hada da sayen kayan tsaro, daukar ma’aikatan tsaron cikin gida, ayyukan tsaro, ma’aikatun tsaro da kuma kudaden asusun tallafawa tsaro.

Bayanai sun nuna cewa kashe kudaden tsaro a jihohin da aka samu bayanansu ya karu sosai, daga Naira biliyan 75.84 a shekarar 2025 zuwa Naira biliyan 252.26 a 2026. Sai dai idan aka kwatanta da shekarar 2025 a jihohin da suke da cikakkun bayanai na shekarun biyu, jihohi 22 ne suka kashe kusan Naira biliyan 144.44 a 2026, idan aka kwatanta da Naira biliyan 75.84 a 2025.

A bangaren nau’in kashe kudaden kuwa, an kashe Naira biliyan 37.08 wajen kayan tsaro, yayin da Naira biliyan 26.89 aka ta tafi zuwa ma’aikatan tsaron cikin gida.

Kudaden tsaro da sauran ayyukan tsaron cikin gida sun tashi daga Naira biliyan 47.67 zuwa Naira biliyan 135.61, yayin da kudaden ma’aikatun tsaro da masu ba gwamnoni shawara kan tsaro suka karu daga Naira biliyan 14.95 zuwa Naira biliyan 42.15.

Haka kuma, kudaden asusun tallafawa tsaro sun karu daga Naira biliyan 6.82 zuwa Naira biliyan 10.53.

Wannan karin kashe kudaden ya zo ne a daidai lokacin da Nijeriya ke ci gaba da fuskantar hare-haren ‘yan bindiga, satar mutane, ta’addanci, kisan gilla da rikice-rikice tsakanin al’umma.

Hukumar kare hakkin dan Adam ta kasa, NHRC, ta ce cibiyar tattara bayanan take hakkin dan Adam ta rubuta rahotannin sace mutane 651 tare da ajalin mutane 492 tsakanin watan Janairu da Maris na 2026.

Rahotanni sun kuma nuna cewa a watan Yuni kadai, mutane 792 sun rasa rayukansu a cikin hare-haren tsaro 882 da aka samu a jihohi 36 da babban birnin tarayya Abuja.

A gefe guda kuma, hukumomin soji da sauran jami’an tsaro sun gudanar da kusan ayyukan yaki da ta’addanci 14,000 a farkon rabin shekarar, inda aka hallaka ‘yan ta’adda da mayakan tawaye 1,597 tare da ceto mutane 1,516 da aka yi garkuwa da su.

Sai dai yawan kudaden da ake kashewa da kuma ci gaba da samun matsalar rashin tsaro ya sake haifar da tambayoyi kan yadda ake amfani da kudaden tsaro da kuma ko suna haifar da sakamakon da ake bukata.

Bayan Kogi, Plateau da Bauchi, Bayelsa ta zo ta hudu da Naira biliyan 17.49, yayin da Ekiti ta kashe Naira biliyan 14.83. Anambra ta kashe Naira biliyan 13.40, Sokoto Naira biliyan 11.27, Ondo Naira biliyan 10.54, sannan Kaduna Naira biliyan 10.37 kamar yadda rahoton na jaridar Punch ya tattaro.

Kazalika rahoton ya ce jihar Kebbi ta kashe Naira biliyan 10.14, Adamawa Naira biliyan 9.95, Zamfara Naira biliyan 9.07, Borno Naira biliyan 8.29, Kano Naira biliyan 8.26, sannan Katsina Naira biliyan 7.21.

Jihar Jigawa kuwa ta kashe Naira miliyan 395.33 a cikin nau’o’in kashe kudaden tsaron da bayanan suka kunsa.

Wasu jihohi hudu, wato Akwa Ibom, Osun, Rivers da Yobe, ba a samu wani kashe kudi a karkashin nau’o’in da aka lissafa ba, yayin da Edo ma ba ta da adadin kudin da aka nuna a teburin.

Jaridar Punch ta ruwaito tsohon jami’in ‘yan sanda, Wilson Inalegwu, ya yi kira ga gwamnoni da su daina ware makudan kudade na tsaro ba tare da bayyana takamaiman shirin yadda kudaden za su rage aikata laifuka ba.

Ya ce ya kamata kwamishinonin ‘yan sanda su rika gabatar da tsare-tsaren aikin ‘yan sanda na shekara, wadanda za su bayyana manyan matsalolin tsaro da ake fuskanta da kuma irin albarkatun da ake bukata wajen magance su.

Inalegwu ya ce hakan zai bai wa gwamnoni damar tantance sakamakon kudaden da aka kashe tare da rike jami’an tsaro da alhakin cimma manufofin da aka tsara.

Shi ma shugaban Centre for Anti-Corruption and Open Leadership, Debo Adeniran, ya ce ‘yan Najeriya suna da hakkin neman cikakken bayani kan yadda ake kashe kudaden tsaro.

Adeniran ya tambayi ko kudaden suna isa ga hukumomin tsaro da jami’an da suke bukatar su, musamman ganin yadda ake ci gaba da samun korafe-korafen rashin isasshen kayan aiki da walwala daga jami’an tsaro.

A nasa bangaren, Daraktan CISLAC, Auwal Musa Rafsanjani, ya bukaci gwamnati ta bayyana inda kudaden suka tafi da kuma irin kayan aiki ko ayyukan da aka samar da su.

Rafsanjani ya ce idan da gaske aka kashe kudaden kamar yadda bayanan suka nuna, ya kamata ‘yan Najeriya su ga ingantaccen sauyi a harkar tsaro.

Ya kuma yi kira ga babban mai binciken kudi na tarayya da ya fitar da cikakken bayani kan kudaden da aka kashe wajen tsaro, ciki har da ayyukan da aka gudanar da kayan aikin da aka saya.

Rahoton na jaridar Punch ya ambato masu sharhi kan harkar tsaro sun bayyana cewa karin kudaden tsaro na iya taimakawa wajen yaki da rashin tsaro, amma sun jaddada cewa samun sakamako na bukatar tsari mai kyau, gaskiya, sahihin amfani da kudade da kuma sa ido mai karfi.

Hakan na nufin cewa babban kalubalen da ke gaban gwamnatocin jihohi ba wai kawai kara yawan kudaden tsaro ba ne, illa tabbatar da cewa kudaden suna haifar da karin tsaro, rage sace-sace da kashe-kashe, tare da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata