Gwamnatin jihar Ondo ta tabbatar da mutuwar mutane 29 sakamakon zargin shan barasa mai guba a ƙaramar hukumar Odigbo da ke jihar.
Jaridar The Sun ta ruwaito cewa kwamishinan lafiya na jihar, Dakta Banji Ajaka, ne ya bayyana hakan a daren Juma’a a birnin Akure, inda ya ce an sami mutane 60 da ake zargin sun kamu da cutar sakamakon wannan lamari.
Ya yi bayanin cewa mutum uku a halin yanzu suna kwance a asibitoci ana ba su kulawa, yayin da wasu mutane 27 ke ƙarƙashin kulawar likitoci ana lura da lafiyarsu.
Ajaka ya ce kashi 95 cikin ɗari na waɗanda lamarin ya shafa maza ne masu shekaru tsakanin 16 zuwa 55, inda aka fi samun lamarin a yankunan Orita Odigbo, Araromi-Obu, Newtown, Odole, Okele, da kuma Oniparaga.
Rahotanni sun bayyana cewa wasu mazauna yankunan da abin ya shafa sun kamu da rashin lafiya ne bayan sun sha wasu abubuwa da ake zargin barasa ce ta gargajiya mai maganin gargajiya (herbal alcoholic drinks).
Kwamishinan ya bayyana cewa alamomin rashin lafiyar sun haɗa da ciwon kai, ciwon jiki, kasala, matsalar gani, wahalar numfashi, da kuma suma ko gushewar hankali, inda halin da wasu marasa lafiyar ke ciki ya taɓarɓare cikin gaggawa.
“Yanayin rashin lafiyar da tarihin shan giya sun haifar da zargi mai ƙarfi na cewa sun sha wata guba da ke cikin barasa. Sai dai har yanzu ba mu sami sakamakon gwajin dakin gwaje-gwaje da ya tabbatar da ainihin abin da ya yi sanadin mutuwar ba,” in ji shi.
Kwamishinan ya ce an karɓi samfuran jini da fitsari guda 36 domin yin gwaji a ɗakin bincike, yayin da aka miƙa samfuran abubuwan da ake zargin barasa ce domin binciken guba.
Ya ce ana gudanar da binciken ne tare da haɗin gwiwar hukumomin da ke kula da ingancin kayayyaki da kuma hukumomin tsaro, inda ya ƙara da cewa an riga an tsare wasu mutane da ake zargi a hannun hukuma.
Ajaka ya ce gwamnatin jihar ta sanya dokar hana samarwa da kuma sayar da barasa ta gargajiya da duk wata barasa mai haɗin maganin gargajiya na wucin-gadi a ƙaramar hukumar da lamarin ya shafa.
Ya buƙaci mazauna yankin da su guji shan kayayyakin barasa da ba su da lasisi, sannan su gaggauta neman kulawar likita idan suka ga matsalar dushewar gani, wahalar numfashi, kasala ba zato ba tsammani, rikicewar tunani, ko kuma suman da ke faruwa bayan shan barasa.
Haka kuma kwamishinan ya yi kira ga mazauna yankin da shugabannin al’umma da su gaggauta kai rahoton duk wata rashin lafiya da ba a saba gani ba ko kuma mutuwar farat ɗaya ga hukumomin lafiya.
Ya tabbatar wa al’umma cewa gwamnati na aiki tare da abokan hulɗa na ƙasa da na ƙasashen duniya domin gano ainihin dalilin mutuwar mutanen da kuma hana ƙarin asarar rayuka.
