DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, September 15, 2026
HomeLabaraiKu yi bayanin sama da biliyan ₦126 da suka bace - SERAP...

Ku yi bayanin sama da biliyan ₦126 da suka bace – SERAP ga INEC

Ƙungiyar SERAP mai fafutikar tabbatar da gaskiya da adalci ta ba hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Nijeriya (INEC) wa’adin kwanaki bakwai da ta gabatar da cikakken bayani kan sama da naira biliyan 126.46 na kuɗin al’umma da aka ware domin gudanar da zaɓe, waɗanda ake zargin an karkatar da su, sun ɓace, ko kuma an yi sama-da-faɗi da su ba tare da bayani ba.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa kiran na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mataimakin daraktan ƙungiyar, Kolawole Oluwadare, ya fitar a ranar Asabar, 12 ga watan Satumban 2026, wadda aka raba wa manema labarai a ranar Lahadi.

Sanarwar ta kafa hujja da rahoton binciken kuɗi na shekarar 2023 daga Babban Odita-Janar na Tarayya da aka fitar a ranar 7 ga watan Agustan 2026, wanda ya shafi binciken kudaden da aka kashe tsakanin Janairu da Disambar 2022, kuma a wasu ɓangarorin ya kai har zuwa 31 ga watan Disambar 2023.

SERAP ta bayyana cewa kuɗaɗen sun shafi sayen akwatunan zaɓe, na’urorin tantance masu kaɗa ƙuri’a, kayayyakin aiki na sirri, da takardun sakamakon zaɓe, tare da sauran hidimomin da suka shafi gudanar da zaɓe a ƙasar.

A cewar rahoton Odita-Janar, INEC ta biya sama da naira biliyan 112 [₦112,155,597,845.00] ba bisa ƙa’ida ba wajen sayen akwatuna da na’urorin zaɓe ba tare da yin sanarwar neman kwangila ba ko samun takardar amincewa daga hukumar BPP, inda ba a sami shaidar cewa an sayo kayayyakin ba, sannan an bai wa kamfanonin da ba a san ƙwarewarsu ko adireshinsu ba kwangilar.

Haka kuma, rahoton ya nuna cewa hukumar ta biya sama da naira biliyan 1 [₦1,058,925,000.00] wajen sayen motocin Toyota Prado TXL na 2021 ba tare da bin ƙa’idar ciniki ba, tare da biyan sama da naira biliyan 3 ga wasu ‘yan kwangila huɗu kafin ma a ba su kwangilar takardun sakamakon zaɓe. Binciken ya ƙara bayyana cewa an rarraba kwangiloli 22 na sama da naira biliyan 9 a rana guda domin kauce wa bin ƙa’idojin sayen kaya, yayin da aka biya sama da naira miliyan 129 ga wasu kamfanonin binciken kuɗi 19 ba tare da shaidar aikin da suka yi ba.

Ƙungiyar ta buƙaci shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, da hukumar baki ɗaya da su gaggauta miƙa batun zuwa ga hukumar yaƙi da yi wa tattalin arziƙi zagon kasa (EFCC) da hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa (ICPC) domin gudanar da bincike, gurfanar da waɗanda ke da hannu, da kuma dawo da kuɗaɗen cikin asusun gwamnati.

SERAP ta gargaɗi hukumar cewa idan har ba ta ɗauki waɗannan matakan ba a cikin kwanaki bakwai, ƙungiyar za ta shigar da ƙara a gaban kotu domin tilasta wa INEC bin doka da kare muradun al’umma.

Ukashatu Wakili
Ukashatu Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili is a journalist and media professional serving as Deputy Managing Editor and Internship Coordinator at DCL Hausa. He has extensive experience in broadcast and digital journalism, with expertise in news reporting, editorial production, newsroom coordination and journalist training. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata