DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Monday, September 21, 2026
HomeSiyasaNDC ta nesanta kanta da kwamitin yaƙin neman zaɓe na OK Movement

NDC ta nesanta kanta da kwamitin yaƙin neman zaɓe na OK Movement

Jam’iyyar NDC ta nesanta kanta daga kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa mai mambobi 59 da ƙungiyar Obi-Kwankwaso Movement, wadda aka fi sani da OK Movement, ta sanar gabannin babban zaɓen 2027.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa jam’iyyar ta kuma gargaɗi cewa babu wani ɗan takara, mutum guda, ko ƙungiyar magoya baya da aka ba ikon kafa ko sanar da wani kwamiti ko tsarin yaƙin neman zaɓe da sunanta ba tare da amincewar kwamitin shugabanni na ƙasa (NWC) ba.

Shugaban jam’iyyar NDC na ƙasa, Sanata Moses Cleopas, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a daren ranar Asabar, kwanaki uku bayan babban daraktan ƙungiyar ta OK Movement, John Ughulu, ya bayyana jerin sunayen kwamitin.

“Shugabancin jam’iyyarmu ta NDC) ya lura da wani bayani da aka danganta ga John Ughulu yana sanar da kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa a ƙarƙashin sunan ‘OK Movement’. Domin kauce wa shakku, jam’iyyar tana mai bayyana cewa ta nesanta kanta ɗari bisa ɗari daga wannan sanarwa. Ba daga jam’iyya ta fito ba, kuma ya kamata al’umma da kafafen yaɗa labarai su yi watsi da ita”, in ji Cleopas.

Shugaban ya ƙara da cewa dukkan ’yan takarar jam’iyyar dole ne su fahimci cewa ba a matsayin ‘yan takara masu zaman kansu suke takara ba, illa dai ’ya’yan jam’iyya ne da ke ƙarƙashin iko da ladabtarwarta, don haka shugabancin jam’iyya ne kaɗai ke da haƙƙin kafa tare da sanar da kwamitin yaƙin neman zaɓe.

Jam’iyyar ta kuma sanar da ɗaukar matakin ladabtarwa a kan Ughulu sakamakon abin da ta kira kutse da wuce gona da iri da ya yi a lokacin zaɓen fidda gwani a jihar Legas da kuma ci gaba da nuna halin ko-in-kula ga ikon jam’iyyar, inda ta miƙa shi ga kwamitin ladabtarwa na jam’iyya domin ɗaukar mataki bisa tanadin kundin tsarin mulkinta.

Sai dai da jaridar Punch  ta tuntuɓi John Ughulu domin jin ta bakinsa, ya soki kalaman Cleopas inda ya bayyana cewa ƙungiyar ta OK Movement mai zaman kanta ce kuma jam’iyyar ba za ta iya tsara mata yadda za ta tafiyar da ayyukanta ba.

Ughulu ya jaddada cewa ƙungiyarsu ba ta ƙarƙashin ikon jam’iyya, domin suna aiki ne kai-tsaye domin biyan buƙatun ’yan takararsu.

Ukashatu Wakili
Ukashatu Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili is a journalist and media professional serving as Deputy Managing Editor and Internship Coordinator at DCL Hausa. He has extensive experience in broadcast and digital journalism, with expertise in news reporting, editorial production, newsroom coordination and journalist training. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata