Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta tabbatar wa ‘yan Nijeriya aniyarta na gudanar da sahihin zaɓe mai cike da gaskiya da riƙon amana gabannin babban zaɓen shekarar 2027.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa shugaban hukumar ta INEC, Farfesa Joash Amupitan (SAN), ya bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin da yake jagorantar ayyuka a ɗakin bibiyar yanayin zaɓe na ƙasa (National Situation Room) da ke hedikwatar hukumar a Abuja.
A cikin wata sanarwa da babban sakataren yaɗa labarai kuma mai ba shugaban INEC shawara kan harkokin kafafen yaɗa labarai, Adedayo Oketola, ya fitar, Farfesa Amupitan ya ce an magance ƙalubalen gudanar da aiki da aka fuskanta cikin hanzari kafin gudanar da zaɓukan cike gurbi a jihohin Gombe, Kano, Bauchi, da Delta.
Amupitan ya bayyana cewa babban aikin ɗakin bibiyar yanayin zaɓen shi ne sanya ido da kuma magance matsaloli kafin su ta’azzara.
“Duk wani ƙalubale na gudanarwa ko na aiki da ya taso kafin ranar zaɓe, hukumar ta yi nasarar magance shi cikin gaggawa. Muna nan a kan bakarmu ta ci gaba da inganta hanyoyin aiki domin duk wani zaɓe da za a yi a gaba ya nuna ƙwarewa mai zurfi tare da ƙara wa al’umma kwarin gwiwa”, in ji sh.
Hukumar ta gudanar da zaɓukan cike gurbi guda huɗu na ‘yan majalisa a ranar Asabar a mazaɓar tarayya ta Gombe/Kwami/Funakaye a jihar Gombe, mazaɓar majalisar dokokin jiha ta Dawakin Kudu a jihar Kano, mazaɓun Sakwa da Disina a jihar Bauchi, da kuma mazaɓar Udu a jihar Delta.
Shugaban INEC ya bayyana waɗannan zaɓukan cike gurbi a matsayin gwajin aiki mai matuƙar muhimmanci da zai samar da darussa masu amfani wajen tunkarar babban zaɓen 2027.
Ya jaddada cewa babu wani zaɓe da ya kamata a ɗauka a matsayin ƙarami ko na yau da kullum, domin kowane zaɓe na bai wa hukumar damar duba tsarin jigilar kayan aiki, gwada ƙarfin na’urorin fasahar zamani, da kuma auna shirye-shiryen jami’ai a filin aiki.
Farfesa Amupitan, tare da kwamishononin INEC na ƙasa da manyan jami’an gudanarwa, sun sanya ido kan yadda zaɓukan suka gudana yayin da ake karɓar rahotanni daga jihohin daban-daban, inda ya yaba wa jami’an ɗakin bibiyar zaɓe, musamman kwararrun kan fasaha, bisa tabbatar da an gudanar da aikin cikin sauƙi ba tare da wata tangarɗa ba.
