DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Monday, September 21, 2026
HomeUncategorized'Masari da ni mun ƙi karɓar N650m don goyon bayan tazarcen Obasanjo'

‘Masari da ni mun ƙi karɓar N650m don goyon bayan tazarcen Obasanjo’

Tsohon shugaban marasa rinjaye a majalisar wakilai ta ƙasa, Farouq Aliyu, ya bayyana cewa ya ƙi karɓar tayin naira miliyan 250 da aka yi masa domin marawa shirin tazarce na uku na tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo baya.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Aliyu ya kuma bayyana cewa kakakin majalisar wakilai na wancan lokacin, Aminu Masari, shi ma ya ƙi karɓar naira miliyan 400 da aka yi masa tayi domin goyon bayan wannan buƙata.

Shirin tazarce na uku yana ɗaya daga cikin manyan batutuwan da suka fi ɗaukar hankali da jawo ce-ce-ku-ce a lokacin mulkin Obasanjo tsakanin shekarar 1999 zuwa 2007, kafin daga bisani a watan Mayun 2006 majalisar dokokin ƙasa ta yi fatali da ƙudirin yi wa kundin tsarin mulki garambawul wanda da ya ba shi damar tsayawa takara a karo na uku a jere, ko da yake tsohon shugaban ya sha musanta neman wannan wa’adi.

Da yake magana a cikin shirin ‘Naija Unfiltered’ da aka saki a YouTube a ranar Juma’a, Aliyu ya jaddada cewa shirin tazarcen gaskiya ne ba ƙage ba. A cewarsa, lokacin da ake tattaunawa kan shirin, tsohon shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa (EFCC), Nuhu Ribadu, ya buƙaci ya je Abuja domin ganawa da Obasanjo.

Tsohon ɗan majalisar ya ce ko da yake da farko ya ƙi amincewa da buƙatar Ribadu, daga baya ya amince ya gana da Obasanjo a Abuja, inda suka tattauna kan batun tazarcen kuma ya tabbatar wa shugaban cewa wannan yunkuri ba zai taɓa yin nasara ba. Ya ƙara da cewa wani mutum da Ribadu ya haɗa shi da shi ne ya yi masa tayin naira miliyan 250, amma bai bayyana sunan mutumin ba yayin tattaunawar.

Aliyu ya ƙara da cewa an yi wa Aminu Masari da shugaban masu rinjaye a lokacin, Abdul Ningi, tayin naira miliyan 400 kowannensu amma suka ƙi karɓa, yayin da sauran ‘yan majalisa aka ba su aƙalla naira miliyan 50 kowannensu.

Haka kuma, tsohon shugaban marasa rinjayen ya bayyana cewa marigayi Muhammadu Buhari, tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar, da sakataren gwamnatin tarayya George Akume, sun taka muhimmiyar rawa wajen daƙile wannan aniya ta tazarce a wancan lokacin.

Ukashatu Wakili
Ukashatu Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili is a journalist and media professional serving as Deputy Managing Editor and Internship Coordinator at DCL Hausa. He has extensive experience in broadcast and digital journalism, with expertise in news reporting, editorial production, newsroom coordination and journalist training. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata