Kamfanin man fetur na Nijeriya NNPCL ya ƙaddamar da rangwamen N66 kan man fetur ga kwastomominsa a faɗin Nijeriya da ke amfani da manhajar NNPC Fuel App.
Kamfanin ya bayyana cewa shirin rangwamen, wanda ya fara ranar 1 ga Oktoba, zai ci gaba har zuwa 7 ga watan, kuma ana gudanar da shi a gidajen mai na NNPC da ke sassa daban-daban na ƙasar.
A wata sanarwa da kamfanin ya wallafa a shafinsa na X ranar Juma’a, NNPC ya ce rangwamen ya riga ya fara gudana, yayin da kwastomomi a wurare daban-daban suka fara cin gajiyar tayin.
Jaridar Punch ta ruwaito kamfanin ya ce hotunan da aka ɗauka a ranar farko ta shirin sun nuna yadda kwastomomi a wasu gidajen man NNPC suka fara amfani da damar da aka samar musu.
NNPC ya kuma ƙarfafa kwastomomi da su ci gaba da sayen man fetur da gudanar da mu’amaloli ta manhajar NNPC Fuel App a tsawon lokacin da rangwamen zai gudana.
Kazalika kamfanin ya ce zai ci gaba da wallafa wasu hotuna da bayanai kan yadda ake gudanar da shirin a gidajen man NNPC da ke faɗin ƙasar, tare da kira ga jama’a da kada su bari damar ta wuce su.
Rangwamen N66 yana samuwa ne ga masu amfani da manhajar NNPC Fuel App a lokacin da aka ware, wato daga ranar 1 zuwa 7 ga Oktoba.
