Sama da malamai Musulmi 1,000 sun yi kira ga shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya janye aniyarsa ta neman sake zaɓe a zaɓen shugaban ƙasa na 2027, bisa abin da suka bayyana a matsayin matsin tattalin arziki, rashin tsaro da sauran ƙalubalen da ke fuskantar ƙasar.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa malaman sun bayyana wannan matsaya ne a cikin wata sanarwar haɗin gwiwa da aka fitar a ƙarshen wani taron ƙasa kan halin da Nijeriya ke ciki a ƙarƙashin gwamnatin Tinubu da kuma babban zaɓen 2027, wanda aka gudanar a jihar Kano ranar Lahadi.
Malaman, waɗanda suka gudanar da taron ƙarƙashin ƙungiyar Ko Da Naka, For the Struggle to Promote Good Governance and Community Development, tare da haɗin gwiwar AFAQ Educational Foundation, sun bayyana rashin gamsuwarsu da yadda suke ganin gwamnatin Shugaba Tinubu ke tafiyar da ƙasar.
A cikin sanarwar, mahalarta taron sun ce wasu daga cikin manufofin tattalin arzikin gwamnatin, ciki har da cire tallafin man fetur, sauye-sauyen tsarin canjin kuɗin Naira, ƙarin kuɗin wutar lantarki da gyare-gyaren haraji, sun ƙara wa talakawa nauyin rayuwa.
Malaman sun yi zargin cewa gwamnati na ci gaba da aiwatar da waɗannan manufofi duk da ƙarin tsadar rayuwa da rashin aikin yi da suke cewa na ci gaba da jefa jama’a cikin ƙunci.
Sun ce ya kamata gwamnati ta sake duba manufofin da suke ganin suna ƙara wa jama’a wahala, maimakon mayar da hankali kan ƙara yawan kuɗaɗen shigar gwamnati.
A cewar sanarwar, mahalarta taron sun amince cewa idan ba a sauya waɗannan manufofin tattalin arziki ba, bai dace a sake zaɓar gwamnatin a zaɓen 2027 ba.
Malamai sun kuma bayyana damuwarsu kan ci gaba da samun kashe-kashe da sace mutane da ayyukan ta’addanci a sassa daban-daban na ƙasar, inda suka buƙaci gwamnati ta ɗauki matakan gaggawa domin magance matsalar tsaro.
Sun fi mayar da hankali kan yankin Arewa maso Yamma da sauran wuraren da matsalar ’yan bindiga da sauran ƙungiyoyin masu aikata laifuka ta yi tsanani.
A cikin sanarwar, malaman sun ce a madadin ci gaba da neman wa’adi na biyu, Shugaba Tinubu ya kamata ya janye takararsa ta 2027.
Sun kuma bayyana cewa idan bai janye takarar ba, alhakin ’yan ƙasa ne su yanke shawarar wanda suke ganin ya fi dacewa su ba wa goyon baya a zaɓen.
Wannan matsayar ta zo ne a lokacin da wasu ƙungiyoyin Musulmi da malaman addini suka bayyana matsaya daban daban, inda wasu daga cikinsu suka nuna goyon baya ga Shugaba Tinubu da aniyarsa ta neman wa’adi na biyu.
A watan Satumban 2026, shugaban ƙungiyar Qadiriyya, Sheikh Qaribullahi Nasiru Kabara, ya bayyana goyon bayan ƙungiyar ga sake zaɓen Tinubu bayan wata ganawa da tawagar kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban kasa na APC ƙarƙashin jagorancin Sanata Abdul’aziz Yari.
Haka kuma, wasu daga cikin manyan ƙungiyoyin Musulmi a Arewa sun gudanar da tattaunawa da tawagar yaƙin neman zaɓen Tinubu, yayin da wasu ƙungiyoyi kuma suka bayyana matsayinsu na goyon bayan shugaban ƙasar.
Daga cikin malaman da suka gabatar da takardu a taron na Kano akwai Dr Abdulmuɗɗalib Ahmad Giɗaɗo, Farfesa Muhd Muslim Ibrahim, Sheikh Kabir Bashir Abdulhamid, Dr Aminu Isma’il Sagagi, Dr Najibullah Abdallah Nuhu da Sheikh Abdurrazaq Uba Musa.
Sauran sun haɗa da Sheikh Musa Muhd Ɗan Kwano, Barrister El-Zubair, Dr Yahuza Getso, Farfesa Ibrahim Siraj Adhama, Dr Umar Dokaji da Sheikh Muhd Sani Khamis, wanda aka fi sani da Abu Haisam.
Yayin da zaɓen 2027 ke ƙara matsowa, batun matsayoyin ƙungiyoyin addini da na sauran masu ruwa da tsaki na ci gaba da zama wani ɓangare na muhawarar siyasar ƙasar, yayin da jam’iyyu da ‘yan takara ke ƙara shirye-shiryen neman goyon bayan jama’a.
