DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Wednesday, October 7, 2026
HomeLabaraiFadar shugaban kasa ta yi watsi da ikirarin cewa wasu ‘ƴan Nijeriya...

Fadar shugaban kasa ta yi watsi da ikirarin cewa wasu ‘ƴan Nijeriya sun tsani Tinubu’

Fadar shugaban kasa ta yi watsi da ikirarin mujallar The Economist cewa ’yan Nijeriya ba sa son Shugaba Bola Ahmed Tinubu, tana mai cewa rahoton bai yi adalci wajen bayyana halin da ƙasar ke ciki da kuma sauye-sauyen tattalin arzikin da gwamnatin ke aiwatarwa ba.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa fadar shugaban kasar ta bayyana matsayarta ne a wata sanarwa da mai ba shugaba Tinubu shawara kan yaɗa labarai Sunday Dare, ya fitar a ranar Talata.

Sanarwar ta zargi mujallar da kallon al’amuran Nijeriya ta hanyar da ba ta nuna cikakken yanayin da ƙasar ke ciki ba.

Fadar shugaban kasar ta ce ikirarin cewa ’yan Nijeriya sun tsani Shugaba Tinubu ba ya bayyana yadda take ganin sauye-sauyen da ake samu a wasu sassa na ƙasar, tana mai cewa wannan ra’ayi ya yi watsi da abin da ta kira manyan matakan gyara da gwamnatin ta fara tun bayan hawanta mulki a watan Mayun 2023.

A cewar sanarwar, ya kamata a fara duba yanayin tattalin arzikin da gwamnatin Tinubu ta tarar kafin a tantance manufofin da ta aiwatar da kuma sakamakonsu.

Fadar shugaban kasar ta ce gwamnatin Tinubu ta gaji tattalin arziki kasar a matsayi mai muni, musamman sakamakon matsalolin tsarin tallafin man fetur, kasuwar canjin kuɗaɗen waje, kuɗaɗen gwamnati da kuma nauyin biyan basussuka.

Ta ce tsarin tallafin man fetur da ya daɗe ana amfani da shi ya janyo asarar makudan kuɗaɗen gwamnati, wanda a cewarta ya kamata a karkatar da su zuwa muhimman fannoni kamar ilimi, kiwon lafiya da ababen more rayuwa.

Fadar ta kuma kare sauye-sauyen da aka yi a tsarin canjin kuɗaɗen waje, tana mai cewa gyaran ya taimaka wajen rage wasu matsalolin da take cewa sun dabaibaye kasuwar kuɗaɗen waje da kuma ƙarfafa harkokin zuba jari.

Sai dai ta amince cewa sauye-sauyen tattalin arzikin sun zo da wani yanayi na wahala ga jama’a, amma ta ce irin wannan matsin lamba ba zai iya zama dalilin dakatar da gyare-gyaren da take ganin suna da muhimmanci ga tattalin arzikin ƙasar ba.

Fadar shugaban kasar ta kuma lissafa asusun ba da lamunin Ilimi na Nijeriya (NELFUND) a cikin shirye-shiryen da take cewa sun taimaka wajen bai wa ɗalibai damar ci gaba da karatu ba tare da ɗaukar nauyin kuɗin makaranta kai tsaye ba.

Haka kuma, ta ce gwamnatin ta samu ci gaba wajen ƙara mafi ƙarancin albashi na ƙasa, tallafa wa sufuri ta hanyar motocin bas masu amfani da iskar CNG, da kuma shirye-shiryen tallafa wa manoma ta hanyar taki, rance da kayan aikin noma.

Gwamnatin Tinubu tace ta tallafa wa batun ’yancin gashin kan kuɗaɗen ƙananan hukumomi, tana mai cewa hakan zai ba hukumomin damar gudanar da ayyukan ci gaba a matakin da ya fi kusa da jama’a.

Ta yi watsi da ikirarin cewa ’yan Nijeriya baki ɗaya suna ƙin Shugaba Tinubu, tana mai cewa akwai wasu ’yan ƙasa da ke ganin tasirin wasu daga cikin shirye-shiryen gwamnati a rayuwarsu.

A cewar fadar shugaban kasa, ɗalibai, ma’aikata, shugabannin ƙananan hukumomi da manoma na daga cikin mutanen da take ganin za su iya bayyana irin tasirin da manufofin gwamnatin ke yi a rayuwarsu.

Sai dai fadar ta amince cewa Nijeriya na fuskantar manyan ƙalubale na tattalin arziki da tsaro, tare da matsin lambar tattalin arzikin duniya da ke shafar ƙasashe daban-daban.

Ta ce duk da waɗannan ƙalubale, gwamnatin Shugaba Tinubu za ta ci gaba da aiwatar da manufofin da ta ce suna da nufin sauya tsarin tattalin arzikin ƙasar da kuma samar da dorewar ci gaban Nijeriya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata