DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Monday, October 12, 2026
HomeSiyasaMun gano Tinubu ne zai lashe zaɓen 2027 — Shugaban APC

Mun gano Tinubu ne zai lashe zaɓen 2027 — Shugaban APC

Jam’iyyar APC ta jaddada cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne zai lashe zaɓen shugaban ƙasa mai zuwa, inda ta bayyana cewa binciken jin ra’ayin jama’a da jam’iyyar ta gudanar ya nuna cewa shugaban na gaba da sauran abokan hamayyarsa.

Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi, yayin da yake zantawa a cikin shirin Sunday Politics na gidan talabijin na Channels Television.

Farfesa Yilwatda ya bayyana cewa Tinubu ya “fi nesa ba kusa ba” idan aka kwatanta shi da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, wanda ke takara a ƙarƙashin jam’iyyar ADC, da kuma Peter Obi na jam’iyyar NDC.

“Mun gudanar da binciken gano gaskiyar lamari kuma muna kan gaba. Muna da namu binciken jin ra’ayin jama’a wanda ke ba mu ainihin ƙididdiga daga dukkan jihohin ƙasar nan,” in ji Yilwatda, yana mai tabbatar da cewa babu shakka APC ce za ta yi nasara.

A cewar shugaban jam’iyyar, APC ba ta fargabar jam’iyyun adawa, domin rashin nasarar da ADC da NDC suka samu a manyan zabukan da suka gabata yana ƙara ba wa jam’iyya mai mulki dama da rinjaye gabanin zaɓen 2027.

Da yake magana kan manufofin tattalin arziƙi, Yilwatda ya ce sabbin dokokin haraji da Shugaba Tinubu ya kawo sun fi taimaka wa talakawa marasa galihu tare da faɗaɗa hanyoyin samun kuɗin shiga ga gwamnati. Ya kuma ƙara da cewa gwamnatin tarayya ta bai wa gwamnatocin jihohi cikakken ikon samarwa da rarraba wutar lantarki.

Dangane da tsadar man fetur da halin da ake ciki a ƙasar, Yilwatda ya bayyana cewa lamari ne na wucin-gadi wanda zai wuce nan ba da jimawa ba, yana mai jaddada cewa ‘yan Nijeriya na da cikakken kwarin gwiwa kan tafiyar gwamnatin APC.

Ukashatu Wakili
Ukashatu Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili is a journalist and media professional serving as Deputy Managing Editor and Internship Coordinator at DCL Hausa. He has extensive experience in broadcast and digital journalism, with expertise in news reporting, editorial production, newsroom coordination and journalist training. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata