DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Saturday, October 17, 2026
HomeSiyasaJam’iyyar ADC ta zargi Kwankwaso da yi wa Tinubu aiki a siyasance

Jam’iyyar ADC ta zargi Kwankwaso da yi wa Tinubu aiki a siyasance

Kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC ya zargi tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, da ciyar da muradun siyasar Shugaba Bola Tinubu gaba, sakamakon kiran da ya yi ga tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, da ya haƙura da takara a 2027 domin ya marawa Peter Obi baya.

Daraktan yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na kwamitin, Kola Ologbondiyan, shi ne ya yi wannan zargi a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a, yayin mayar da martani kan hirar da Kwankwaso ya yi da gidan talabijin na Channels.

Ologbondiyan ya bayyana matakin Kwankwaso a matsayin wanda ya shafi muradun kansa, kuma zai iya ƙara rura wutar rarrabuwar kawuna a tsakanin ’yan adawa, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

 

Mai magana da yawun kwamitin ya tambayi dalilin da ya sa Kwankwaso ke karkata hankalinsa ga shugabannin ’yan adawa maimakon sukar gwamnatin Tinubu, wadda a cewar sa, ’yan Nijeriya ke ɗokin sauya ta saboda matsin tattalin arziki, yunwa, talauci da rashin tsaro.

Kakakin ya nuna cewa matsayin Kwankwaso na iya kasancewa yana da alaƙa da burinsa na siyasa bayan zaɓen 2027. Ya zarge shi da fi mayar da hankali kan yadda zai shirya tsaf domin takarar shugaban ƙasa a 2031, maimakon gina haɗin kan ’yan adawa.

Ya kuma yi nuni da rahotannin da suka danganta Kwankwaso da bayyana matsayin mataimakin shugaban ƙasa a matsayin “spare tyre”, inda ya ce sabon matakin da ya ɗauka ya haifar da tambayoyi kan ainihin manufarsa a wannan fafatawar siyasa.

Kwamitin ya kuma yi watsi da ra’ayin cewa goyon bayan Kwankwaso shi ne ginshiƙin da duk wani ɗan takara ke buƙata domin samun nasara a zaɓen jihar Kano, wadda ita ce cibiyar siyasarsa.

Ologbondiyan ya yi nuni da zaɓen shugaban ƙasa na 2003 da 2007, inda ya ce tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya samu nasara a Kano ba tare da goyon bayan Kwankwaso ba, don haka Atiku ma zai iya samun gindin zama a jihar a zaɓen 2027.

Ya ƙara da cewa ’yan Nijeriya ba za su bari a karkatar da hankalinsu da abin da ya kira dabarun siyasa da ake amfani da su wajen raunana jam’iyyun adawa gabanin babban zaɓe na gaba ba.

Ologbondiyan ya kuma yi tambayoyi kan sauye-sauyen da Kwankwaso ya riƙa yi a tafiyar siyasarsa, inda ya bayyana sauya sheƙarsa daga jam’iyyar PDP zuwa APC, komawa PDP, sannan ya bi ta jam’iyyar NNPP da wasu dandamalin ’yan adawa, a matsayin abin da ya kamata a bincika.

Kakakin ADC-PCC ya kuma ƙalubalanci ikirarin Kwankwaso na cewa yana da babban tasiri a siyasar ƙasa baki ɗaya, yana mai nuni da cewa ya zo na huɗu a zaɓen shugaban ƙasa na 2023.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata