DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Kwamishinan Jigawa ya mayar da rarar Naira miliyan 301 daga kudaden da aka ware don shirin ciyar da al’umma a watan Ramadan

-

Kwamishinan ayyuka na musamman na jihar Jigawa, Alhaji Auwalu Danladi Sankara, ya mayar da Naira miliyan 301 zuwa baitul malin jihar, daga cikin Naira biliyan 4 da miliyan dari 800 na kasafin kudin shirin ciyar da al’umma a watan Ramadan.

A yayin wata gajeriyar liyafa a Dutse babban birnin jihar, kwamishinan ya bayyana cewa bayan aiwatar da shirin ciyar da jama’a yadda ya kamata, an samu ragowar kuɗi, kuma saboda gaskiya da amana, ya mayar da su domin al’umma.

Google search engine

Kungiyoyin fararen hula da al’umma sun bayyana jin daɗin su da wannan ɗabi’a ta gaskiya daga Kwamishina Sankara, tare da kiran sauran jami’an gwamnati da su yi koyi da irin wannan tsari na adalci da gaskiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Adadin mutanen da suka rasa rayukansu a hatsarin Kwale – kwale a Yobe ya karu zuwa 29

Adadin mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon hatsarin kwale-kwale da ya faru a karamar hukumar Nguru ta jihar Yobe ya ƙaru daga 25 zuwa 29,...

Kungiyar likitoci masu neman kwarewa za ta tsunduma sabon yajin aiki

Kungiyar Likitocin masu neman kwarewa NARD ta bayyana cewa za ta tsunduma yajin aikin sai baba ta gani daga Litinin, 12 ga Janairu, 2026, sakamakon...

Mafi Shahara