DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Gwamnatin jihar Anambra ta haramta bara

-

Gwamnatin jihar Anambra ta haramta raba kayan abinci da sauran kyaututtuka ga mabarata a tituna da wuraren taruwar jama’a.

Gwamnatin jihar ta ware musamman karkashin gadar Aroma da ke Awka, babban birnin jihar, da sauran wurare a matsayin manyan wuraren da ta hana wannan dabi’a.

Google search engine

Haka kuma, gwamnatin jihar ta haramta kowace irin bara, yawo ba gaira ba dalili da kuma kasuwanci a kan titi a karkashin gadar Awka, tana mai cewa wannan mataki ya zama dole don kare mutunci da tsari na babban birnin, wanda ke wakiltar fuskar jihar.

Wata sanarwa da Darakta Janar kuma Shugaba na Hukumar Raya Birnin Babban Birnin Jihar Anambra Anambra State Capital Territory Development Authority, Ossy Onuko, ya fitar, ta bayyana cewa wannan umarni na daga cikin kokarin gwamnati na tsaftace birnin da kuma tabbatar da doka da oda.

Onuko ya ce duk wanda aka samu da karya wannan umarni za a kama shi tare da gurfanar da shi a gaban kotu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Har yanzu bamu kammala bincike ba shiyasa bamu gurfanar da El-rufa’i a gaban kotu ba – EFCC

Hukumar EFCC, mai yaki a cin hanci da rashawa a Nijeriya ta bayyana dalilin da ya sa har yanzu ba ta kai tsohon gwamnan Kaduna,...

Wanene sabon Shugaban Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya, Olatunji Disu?

AIG Olatunji Disu ya kasance gogaggen jami’i wanda aka nada don jagorantar rundunar 'yan sandan kasar a matsayin IGP na 23. A cewar fadar shugaban...

Mafi Shahara