Sunday, April 5, 2026
HomeLabaraiZa a fara cire kudin amfani da bankuna ta USSD kai tsaye...

Za a fara cire kudin amfani da bankuna ta USSD kai tsaye daga katin kiran waya na layikan kwastomomi a Najeriya

Daga Larabar nan 18 ga watan Yuni, 2025, kamfanonin sadarwa a Najeriya za su fara cire N6.98 kai tsaye daga layin masu amfani da Bankuna a kowane daƙiƙa 120 na amfani da USSD.

An bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da Shugaban Ƙungiyar Kamfanonin Sadarwa masu lasisi a Najeriya (ALTON), Gbenga Adebayo, da Sakataren Yaɗa Labaranta, Damian Udeh, suka sanya wa hannu.

Kungiyar ALTON ta ce tsarin na hadin gwiwa ne da hukumar sadarwa ta kasa NCC da babban bankin Nijeriya CBN.

Rahoton Jaridar Daily Nigerian ya tattaro cewa kwastomomi za su samu sakon amincewa kafin a cire kudin, kuma ba zai shafi ayyukan banki na USSD ba muddin akwai airtime.

USSD services: Telcos to charge subscribers directly from June 18

RELATED ARTICLES

2 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata