Kwamishinan Lafiya na Legas, Farfesa Akin Abayomi, ya ce kashi 95% na masu zazzabi a jihar ba maleriya ke haddasa musu ba.
Ya ce hakan na sa mutane su rika amfani da magungunan maleriya da na ƙwayoyin cuta ba tare da gwaji ba, abin da ke haifar da cututtuka masu jure magani.
Rahoton Jaridar Punch ya ce a don haka ne, gwamnatin ta bullo da tsarin “gwaji, magani da sa ido” domin dakile matsalar. Ya kuma jaddada haramcin sayen magani ba tare da takardar izini daga likita ba.
Farfesa Wellington Oyibo ya ce rashin gwaji na haddasa mutuwa, musamman ga yara. Ya kuma ce Legas na bukatar sahihan bayanai don cin nasarar yakar maleriya.
