Ba za a taɓa samun ɗan wasan da ya kai Messi a harkar kwallo ba – Xavi Hernández
Tsohon ɗan wasan tsakiyar FC Barcelona Xavi Hernández, ya yabawa Messi kan bajintar da ya nuna a harkar ƙwallon ƙafa, inda ya ce ya shafe shekaru 15 yana taka leda tare da Messi a Barcelona kuma ya shaida irin kwarewar da yake da ita a kowanne fanni na wasa.
A wata hira da ya yi, Xavi ya ce Messi ya fi dukkan ‘yan wasan da ya taɓa gani ko taka leda tare da su, har da Neymar.
Xavi ya ce bai taba tsammanin a ƙwallon ƙafa za a sake samun wani ɗan wasa irin Messi ba, inda ya yi fatan a sake samun wanda ya fi Messi amma ya ce zai yi wuyar samu.
