Majalisar Dattawan Nijeriya ta bayyana cewa ba a saka Abuja cikin tsarin kafa ‘yan sandan jihohi ba, saboda yankin ba shi da gwamna ko majalisar dokokin jiha da za su tafiyar da irin wannan tsarin.
Shugaban kwamitin majalisar dattawa kan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a, Yemi Adaramodu, ne ya bayyana hakan yayin da yake magana da jaridar Punch a ranar Juma’a kan dalilin da ya sa birnin na Abuja ba ya cikin tsarin da aka tanada a kundin tsarin mulkin ƙasar domin kafa ‘yan sandan jihohi.
Adaramodu ya ce tsarin gudanar da birnin tarayyar ya bambanta da na jihohi 36 na ƙasar, domin gwamnatin tarayya ce ke da alhakin gudanar da yankin kai tsaye. Ya bayyana cewa minista ne ke jagorantar Abuja, kuma yana aiki a ƙarƙashin majalisar zartarwa ta tarayya.
A cewar ɗan majalisar daga Ekiti, Abuja ba ta da majalisar dokokin jiha kamar sauran jihohin ƙasar. Maimakon haka, majalisar dokokin Nijeriya ce ke da ikon yin dokoki da suka shafi yankin babban birnin tarayya.
Ya ce saboda wannan tsarin na musamman, ‘yan sandan tarayya ne za su ci gaba da kasancewa masu kula da harkokin tsaro da aikin ‘yan sanda a FCT, maimakon kafa rundunar ‘yan sanda ta musamman da za ta kasance ƙarƙashin tsarin ‘yan sandan jihohi.
Wannan bayani ya zo ne a daidai lokacin da gwamnatin Nijeriya ke shirin sake fasalin tsarin aikin ‘yan sanda, sakamakon ƙarin kiraye-kirayen a raba ikon kula da ‘yan sanda daga matakin tarayya tare da bai wa jihohi damar kafa nasu rundunonin ‘yan sanda.
Fadar shugaban ƙasa ta sanar da cewa ana sa ran Shugaba Bola Tinubu zai karɓi daftarin dokar zartarwa kan sabon tsarin ‘yan sanda na ƙasa a ranar 3 ga Satumba, a matsayin wani mataki na sake fasalin tsarin aikin ‘yan sanda a Nijeriya.
Shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa kuma shugaban ƙungiyar da ke aiki kan dokar sabon tsarin ‘yan sanda ta ƙasa, Femi Gbajabiamila, ne ya bayyana hakan bayan wata ganawa da ƙungiyar ta gudanar a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.
Gbajabiamila ya kuma bayyana samar da wata kafa ta musamman ta yanar gizo da ‘yan Nijeriya za su iya amfani da ita wajen gabatar da shawarwari da takardun korafe-korafen da za su taimaka wajen tsara dokar kafin shugaban ƙasa ya duba ta, sannan a miƙa ta majalisar dokokin Nijeriya domin ci gaba da aikin dokoki.
A ƙarƙashin gyaran kundin tsarin mulkin da aka gabatar, majalisun dokokin jihohi za su samu ikon yin dokoki da suka shafi kafa wa, tsarin gudanarwa, samar da kuɗaɗe da kuma sa ido kan rundunonin ‘yan sandan jihohinsu.
Tsarin ya kuma tanadi cewa jihohi ne za su ɗauki babban nauyin samar da kuɗaɗen gudanar da rundunonin ‘yan sandan nasu, yayin da gwamnatin tarayya za ta iya bayar da tallafi ko gudummawar kuɗi ga jihohin bisa wasu sharudda.
Wani sabon tanadi, sashe na 216A, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya za ta iya bai wa ‘yan sandan jihohi tallafi ko gudummawa bisa shawarar majalisar ‘yan sanda ta ƙasa, sannan da amincewar majalisar dokokin Nijeriya.
Sai dai tsarin bai fayyace takamaiman kaso ko mafi ƙarancin kuɗin da gwamnatin tarayya za ta bayar ba, haka kuma bai samar da wata ƙayyadaddiyar hanyar samun kuɗaɗen da za a tabbatar da su kai tsaye ga rundunonin ‘yan sandan jihohi ba.
Wannan na nufin jihohi za su kasance masu ɗaukar babban nauyin kuɗaɗen rundunonin ‘yan sandansu, yayin da samun tallafin gwamnatin tarayya zai dogara ne kan shawarar majalisar ‘yan sanda ta ƙasa da kuma amincewar majalisar dokokin Nijeriya.
Majalisar ‘yan sanda ta ƙasa, wadda shugaban ƙasa ke jagoranta tare da wasu manyan jami’an gwamnatin tarayya da na jihohi, za ta iya taka muhimmiyar rawa wajen tsara dangantakar kuɗaɗe da gudanarwa tsakanin jihohi da gwamnatin tarayya idan sabon tsarin ya fara aiki.
