DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, September 15, 2026
HomeSiyasaADC ta ce ta hada kai da jam'iyyar Accord domin hana APC...

ADC ta ce ta hada kai da jam’iyyar Accord domin hana APC yin nasara a zaɓe Osun

Jam’iyyar ADC ta bayyana cewa ta haɗa gwiwa da jam’iyyar Accord a zaben gwamnan jihar Osun da aka gudanar ranar 15 ga watan Agustan 2026, da nufin hana jam’iyyar APC sake kwace mulki a jihar.

Sakataren yada labarai na ADC na kasa, Bolaji Abdullahi, ne ya bayyana hakan yayin wata hira da gidan talabijin na Trust TV, inda ya yi karin haske kan yadda jam’iyyar ta yi rawar gani a wannan zaben.

A zaben, dan takarar ADC na gwamna, Najeem Salaam, ya samu kuri’u 17,180, yayin da gwamnan jihar kuma dan takarar Accord, Ademola Adeleke, ya lashe zaben da kuri’u 511,067.

Adeleke ya doke babban abokin hamayyarsa, Bola Oyebamiji na jamiyyar APC, wanda ya samu kuri’u 444,815.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito Abdullahi ya ce ADC ta yi hasashen cewa rarrabuwar kuri’un ‘yan adawa na iya bai wa APC damar samun nasara, lamarin da ya sa ta ga bukatar hada kai da Accord tun kafin zaben.

Ya bayyana cewa hadin gwiwar jam’iyyun adawar ya kasance matakin da shugabancin ADC ya amince da shi, domin tabbatar da cewa kuri’un ‘yan adawa ba su warwartse ba.

A cewarsa, ADC ba ta kallon rashin nasarar dan takararta a matsayin gazawa, saboda babban burin jam’iyyar shi ne ganin APC ba ta sake dawowa kan mulki a Osun ba.

“Saboda haka, nasarar da muka samu ita ce ganin an kayar da APC. Ba mu dauki rashin nasarar dan takararmu a matsayin faduwa ko gazawa ba,” in ji shi.

Abdullahi ya kuma bayyana cewa ADC ba za ta ce ita ce kadai ta samar da nasarar Adeleke ba, yana mai cewa yabo da nasarar sun fi dacewa su tafi ga al’ummar jihar Osun.

Ya ce nasarar zaben ta nuna cewa idan jam’iyyun adawa suka hada kai, za su iya kayar da jam’iyya mai mulki a babban zaben 2027.

A cewarsa, abin da ya faru a Osun ya zama wata shaida cewa hadin kan ‘yan adawa na iya sauya sakamakon zabe, duk da karfin jam’iyyar da ke kan mulki.

Hakan na zuwa ne yayin da ake kara samun yunkurin hada kan wasu manyan jam’iyyun adawa domin tunkarar jam’iyyar APC a zaben shugaban kasa na 2027.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata