Jam’iyyar ADC ta zargi wasu masu hannu a gwamnati da ƙoƙarin matsa wa alƙalai lamba domin su janye daga sauraron shari’ar rikicin shugabancin jam’iyyar da Nafiu Bala Gombe ya shigar.
A wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran jam’iyyar na ƙasa, Mallam Bolaji Abdullahi, ya fitar, ADC ta ce ta gano wani shiri na matsa wa Mai shari’a Emeka Nwite ya janye daga shari’ar domin a mayar da ita hannun wasu alƙalan da ake ganin za su iya yin biyayya ga tasirin siyasa.
Jam’iyyar ta bayyana lamarin a matsayin barazana ga ’yancin kai da mutuncin ɓangaren shari’a a Nijeriya.
ADC ta ce duk da cewa har yanzu ba a fitar da cikakken kwafen hukuncin Kotun Ƙoli ba, abin mamaki ne yadda aka sanya ranar 8 ga Mayun 2026 domin ci gaba da sauraron shari’ar.
Jam’iyyar ta ce tana da dalilan da suka sa take zargin cewa ana ƙoƙarin tilasta wa Mai shari’a Nwite ya janye daga shari’ar domin a bai wa wani alkali daban.
A cewar ADC, wannan ya saɓa wa umarnin Kotun Ɗaukaka Ƙara da Kotun Ƙoli da suka bukaci a gaggauta sauraron shari’ar a gaban alkali mai sauraron ta tun farko.
Jam’iyyar ta ce duk wani yunƙuri na cire shari’ar daga hannun Mai shari’a Nwite ta hanyar matsin lamba ko barazana na nufin tsoma baki cikin harkokin shari’a.
Saboda haka ADC ta yi kira ga Majalisar Shari’a ta Ƙasa (NJC) da Babban Alƙalin Nijeriya da sauran masu ruwa da tsaki a ɓangaren shari’a su shiga lamarin domin kare mutuncin kotuna.
