DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, September 22, 2026
HomeWasanniRonaldo ya ci ƙwallo ta 100 a firimiyar Saudiyya

Ronaldo ya ci ƙwallo ta 100 a firimiyar Saudiyya

Fitaccen ɗan wasan Al Nassr, Cristiano Ronaldo, ya ci ƙwallo 100 a gasar firimiyar Saudiyya bayan da ƙungiyarsa ta doke Al Shabab da ci 4-2.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Ronaldo mai shekara 41 ya ci ƙwallonsa ne a minti na 75 a wasan da aka buga ranar Alhamis a filin King Saud University Stadium.

Tauraron ɗan wasan ya zama ɗan wasa na farko daga ƙasashen waje da ya kai ƙwallo 100 a gasar Saudiyya tun bayan zuwansa ƙungiyar Al Nassr a Janairun 2023.

Rahoton ya ce João Felix ɗan ƙasar Portugal shi ma ya ci hat-trick a wasan, sai dai nasarar Ronaldo ta fi jan hankali saboda sabon tarihin da ya kafa.

Ƙwallon da Ronaldo ya ci ita ce ta 26 da ya zura a wannan kakar, kuma yanzu ya zura ƙwallo a ragar dukkan ƙungiyoyin gasar Saudiyya a kakar bana.

Wannan ne karo na biyu a tarihin Ronaldo da ya ci ƙwallo a kan dukkan ƙungiyoyin gasar cikin kaka guda, bayan irin wannan bajintar da ya yi a Real Madrid a kakar 2011/2012.

Rahoton ya ƙara da cewa Ronaldo yanzu shi ne kaɗai ɗan wasa da ya kai ƙwallo 100 a ƙungiyoyi huɗu daban-daban da suka haɗa da Manchester United, Real Madrid, Juventus da Al Nassr.

Nasarar ta sa Al Nassr ta ci gaba da jan ragamar teburin gasar da maki 82 daga wasa 32, maki biyar a gaban Al Hilal.

Ukashatu Wakili
Ukashatu Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili is a journalist and media professional serving as Deputy Managing Editor and Internship Coordinator at DCL Hausa. He has extensive experience in broadcast and digital journalism, with expertise in news reporting, editorial production, newsroom coordination and journalist training. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata