Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ya sake tabbatar da goyon bayansa ga shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, domin ya sake neman wa’adin mulki na biyu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Adeleke ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da ya gudanar ranar Lahadi, jim kaɗan bayan hukumar INEC ta ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan Osun na ranar 15 ga Agusta.
Gwamnan ya yaba wa Shugaba Tinubu kan abin da ya bayyana a matsayin goyon bayansa wajen tabbatar da gudanar da zaɓen Osun cikin ’yanci da adalci.
Adeleke ya ce: “Shugaba Tinubu ɗan jihar Osun ne, kuma ina sake tabbatar da goyon bayana na gare shi domin ya sake tsayawa takarar wa’adin mulki na biyu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.”
Gwamnan ya riga ya bayyana goyon bayansa ga Tinubu a baya, duk da cewa a wancan lokacin yana cikin jam’iyyar PDP, kafin daga bisani ya koma jam’iyyar Accord domin ya sake neman kujerar gwamnan Osun.
INEC ta ayyana Adeleke a matsayin wanda ya lashe zaɓen da misalin ƙarfe 7:24 na safe ranar Lahadi, bayan ya samu ƙuri’u 511,067.
Ya doke ɗan takarar APC, Bola Oyebamiji, wanda ya samu ƙuri’u 444,815, yayin da ɗan takarar ADC, Najeem Salaam, ya zo na uku da ƙuri’u 17,180.
Adeleke ya yi nasara a ƙananan hukumomi 19 daga cikin 30 na jihar, yayin da Oyebamiji ya samu nasara a ƙananan hukumomi 11.
Bayan ayyana sakamakon, Adeleke ya kuma gode wa Shugaba Tinubu bisa kiran da ya yi masa domin taya shi murnar nasarar da ya samu.
Ya ce yana fatan Oyebamiji zai ma taya shi murna, yana mai jaddada cewa “babu mai nasara, babu wanda ya sha kashi”, domin zaɓe ya wuce kuma yanzu abin da ya fi muhimmanci shi ne ci gaban jihar.
Adeleke ya ce: “Ina so in yi amfani da wannan dama wajen gode wa Shugaban Kas, ya kira ni kuma ya taya ni murna, ina gode maka, Shugaban Kasa, saboda tabbatar da cewa dimokuraɗiyya ta ci gaba da aiki a Nijeriya.”
