Tsohon mataimakin shugaban Nijeriya kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya yi zargin cewa akwai wani sabon shiri da wasu masu ruwa da tsaki a gwamnatin Tinubu ke yi na hana jam’iyyar ADC shiga zaɓen shekarar 2027.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Phrank Shaibu, ya fitar ranar Litinin, inda ya ce Atiku ya samu sahihan bayanai da ke nuna cewa ana ƙoƙarin amfani da hanyoyin siyasa da shari’a domin hana ADC kasancewa cikin jam’iyyun da za su fafata a zaɓen 2027.
Atiku ya ce sun san irin waɗannan shirye-shiryen, yana mai abinda akeso shine hana ADC shiga zaɓe saboda ita ce mafi ƙarfi da ke samun karɓuwa a tsakanin ‘yan Nijeriya.
Ya yi kira ga al’ummar ƙasar da su tsaya tsayin daka wajen kare dimokuraɗiyya tare da ƙin amincewa da duk wani yunƙuri na zaɓar wa jama’a jam’iyyun da za su iya kaɗa wa ƙuri’a.
Ya ƙara da cewa abubuwan da suka faru a baya-bayan nan sun nuna yadda ake amfani da hukumomin gwamnati da kotuna wajen matsa wa jam’iyyun adawa lamba, ta hanyar ƙirƙirar rikice-rikice, shari’o’in da ba su da tushe da kuma wasu matakan gudanarwa domin raunana su.
A cewarsa, maimakon gwamnati ta mayar da hankali kan matsalolin da suka addabi ƙasa kamar tsadar rayuwa, rashin tsaro, rashin aikin yi da hauhawar farashi, ta fi mayar da hankali kan yadda za ta ci gaba da riƙe mulki.
Atiku ya bayyana cewa abin da ya kamata gwamnati ta yi shi ne ta fito da manufofi masu kyau domin neman amincewar masu zaɓe, ba yin amfani da kotuna ko hukumomin gwamnati wajen hana jam’iyyun adawa shiga zaɓe ba.
Ya ce duk wani yunƙuri na hana ADC shiga zaɓen 2027 zai zama babban barazana ga dimokuraɗiyyar Nijeriya.
Ya kuma yi kira ga ɓangaren shari’a da ya kasance mai zaman kansa, tare da roƙon INEC, hukumomin tsaro, ƙungiyoyin farar hula da ƙasashen duniya su sanya ido kan duk wani mataki da zai iya kawo cikas ga sahihancin zaɓen 2027.
A ƙarshe, Atiku ya ce dimokuraɗiyya tana bunƙasa ne idan al’umma ba su yi shiru ba, yana mai jaddada cewa ikon zaɓar shugabanni mallakin ‘yan Nijeriya ne, ba na masu riƙe da madafun iko ba.
