DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, July 7, 2026
HomeLabaraiRundunar sojin Nijeriya ta yi bikin cika shekara 163

Rundunar sojin Nijeriya ta yi bikin cika shekara 163

Rundunar sojin Nijeriya ta sake tabbatar da kudirinta na kare martabar kasar tare da ci gaba da yakar ta’addanci, garkuwa da mutane, fashi da makami da sauran matsalolin tsaro yayin bikin cika shekaru 163 da kafuwarta.

Babban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Olufemi Oluyede, ne ya bayyana hakan a wani sakon fatan alheri da aka karanta a madadinsa yayin taron addu’ar mabiya addinin Kirista na bikin ranar rundunar sojin Nijeriya ta shekarar 2026 da aka gudanar a Abuja.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Manjo Janar Maxwell Dangana ne ya wakilci hafsan sojin, inda ya bayyana bikin a matsayin damar gode wa Allah, nazari kan tafiyar rundunar, tunawa da nasarorin da aka samu da kuma girmama jami’an da suka sadaukar da rayuwarsu wajen kare kasa.

Oluyede ya ce taken bikin bana mai taken “Kare Kasa da Bautawa Jama’a: Mataki na Gaba ga Rundunar Sojin Nijeriya” na nuna nauyin da kundin tsarin mulki ya dora wa rundunar wajen kare rayuka da tabbatar da zaman lafiya.

Ya ce har yanzu sojoji na ci gaba da gudanar da ayyuka a yankuna daban-daban domin yakar ‘yan ta’adda, masu garkuwa da mutane, masu satar mai da sauran masu aikata laifuka.

A cewarsa, rundunar ta samu gagarumar nasara ta hanyar hallaka masu aikata laifuka, rusa maboyar ‘yan ta’adda da kubutar da mutane da aka yi garkuwa da su.

Hafsan sojin ya bayyana cewa rundunar ta samu karin masu neman shiga aikin soja bayan umarnin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na kara karfafa tsarin tsaron kasar.

Ya ce sabon tsarin zai taimaka wajen kara yawan jami’ai domin tinkarar matsalolin tsaro yadda ya kamata.

Oluyede ya kuma tabbatar da cewa za a horas da sabbin sojojin tare da samar musu kayan aiki da horo na zamani.

A hudubar da ya gabatar, Daraktan kula da limaman Katolika na rundunar sojin Nijeriya, Birgediya Janar Anthony Maimagani, ya bayyana aikin soja a matsayin kira daga Allah domin kare kasa da al’umma.

Ya bukaci jami’ai su rika mutunta rayukan ‘yan kasa tare da gudanar da aiki cikin gaskiya, tausayi da kishin kasa.

Ukashatu Wakili
Ukashatu Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata