DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, July 7, 2026
HomeKetareFarashin ɗanyen man fetur ya tashi bayan sabon rikici tsakanin Iran da...

Farashin ɗanyen man fetur ya tashi bayan sabon rikici tsakanin Iran da Amurka

Farashin danyen mai a kasuwannin duniya ya fara tashi a ranar Litinin bayan sabon rikicin soji tsakanin ƙasashen Iran da Amurka ya ƙara tayar da hankalin masu zuba jari kan tsaron zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigin ruwan Strait of Hormuz, wanda ke da matuƙar muhimmanci wajen jigilar man fetur na duniya.

Rahotanni sun bayyana cewa sabon rikicin ya biyo bayan hare-haren soji tsakanin Iran da Amurka, lamarin da ya janyo fargabar cewa zirga-zirgar jiragen dakon mai ta mashigin Hormuz na iya fuskantar cikas.

Mashigin Hormuz na daga cikin manyan hanyoyin jigilar man fetur a duniya, inda kusan kashi ɗaya cikin biyar na danyen man da ake safararsa ke bi ta wannan hanya, duk wata barazana ga tsaronsa na iya haddasa tashin farashin mai a kasuwannin duniya.

Masana tattalin arziki sun ce wannan sabon rikici ya sa masu zuba jari suka fara nuna damuwa kan yiwuwar ƙarancin samar da mai idan rikicin ya ƙara tsananta.

Idan rikicin ya ci gaba, ana sa ran farashin man fetur zai iya ƙara hauhawa, lamarin da ka iya shafar farashin makamashi da kayayyaki a ƙasashe da dama, ciki har da Nijeriya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata