Tsohon mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Aminu Abdulsalam Gwarzo, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar ADC.
Gwarzo ya bayyana hakan ne a cikin wata takardar murabus mai dauke da kwanan wata 1 ga Mayu, 2026, wadda ya aika wa Shugaban jam’iyyar ADC a karamar hukumar Gwarzo ta jihar Kano, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
A cikin takardar, tsohon mataimakin gwamnan ya ce murabus dinsa ya fara aiki nan take, inda ya danganta hakan da sabbin sauye-sauyen siyasa da kuma bukatar sake duba matsayinsa a jam’iyyar bisa ga hangen nesansa na siyasa.
Ya bayyana cewa matakin da ya dauka ya samo asali ne daga abin da ya kira kishin kasa da kuma burin bin tafarkin siyasa da ya dace da akidunsa.
Tsohon mataimakin gwamnan ya gode wa shugabanni da ‘ya’yan jam’iyyar bisa goyon bayan da suka ba shi a lokacin da yake cikinta.
