DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Wednesday, May 13, 2026
HomeSiyasaKu biyo mu NDC don kawar da gwamnatin Tinubu - Buba Galadima...

Ku biyo mu NDC don kawar da gwamnatin Tinubu – Buba Galadima ga Atiku

Wani jigo a jam’iyyar NDC Buba Galadima, ya bukaci tsohon mataimakin shugaban Nijeriya Atiku Abubakar, da ya koma jam’iyyar domin karfafa hadin kan ‘yan adawa gabanin zaben 2027.

Galadima ya bayyana hakan ne yayin da ya fito a matsayin bako a shirin ‘Politics Today’ na gidan talabijin din Channels.

Ya ce manyan ‘yan adawa sun fara hadewa karkashin jam’iyyar NDC domin samar da karfi mai iya kalubalantar jam’iyyar mai mulki ta APC.

A cewarsa, akwai damuwa cewa gwamnatin da ke kan mulki na iya amfani da hanyoyin shari’a domin raunana kokarin ‘yan adawa, lamarin da ya sa ya zama dole su hade a wuri guda.

Galadima ya gargadi cewa idan Atiku ya ki shiga jam’iyyar, za a iya dora masa alhakin duk wata gazawa wajen hada kan ‘yan adawa kafin zaben 2027.

Ya kara da cewa hukuncin na hannun tsohon mataimakin shugaban kasar ne, amma ya kamata ya shiga cikin wannan yunƙuri domin cimma burin kawar da gwamnatin APC.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata