DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, September 22, 2026
HomeLabaraiAmnesty international na bukatar ƙwaƙƙwaran bincike kan mutuwar matasa 37 a Niger 

Amnesty international na bukatar ƙwaƙƙwaran bincike kan mutuwar matasa 37 a Niger 

Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International na kiran gaggawa ga hukumomin Nijeriya su kafa kwamitin bincike mai zaman kansa kan mutuwar matasa 37, ciki har da kananan yara, da suka rasu a hannun jami’an Hukumar tsaro na Civil Defence Jihar Neja.

A wata sanarwar da Amnesty ta sanya a shafinta na facebook ta ce, an ce an kama wadanda abin ya shafa ne a ranakun 15 da 16 ga Satumba 2026 a wuraren hakar ma’adinai da ke yankin M.I. Wushishi/Lukoto na Minna.

Wannan kiran na neman bincike ne domin gwamnati ta gano yadda tsare mutanen na tsawon kwana daya zuwa biyu ya rikide ya zama bala’in da ya yi sanadin mutuwar mutane 37, ciki har da kananan yara.

A cewar Amnesty international, ya kamata binciken ya kasance cikin gaggawa, cikakke, mai zaman kansa, ba tare da son rai ba, kuma a gudanar da shi cikin gaskiya da adalci.

Wadanda bincike ya tabbatar da cewa suna da hannu wajen haddasa wannan mummunan lamari bai kamata a hukunta su da matakan ladabtarwa na cikin gida ko na gudanarwa kawai ba inji Amnesty, kamata ya yi su fuskanci cikakken hukuncin doka.

Kungiyar ta kara hakkin ɗan Adam a Nijeriya ta kuma ce ya zama dole a fito fili a bayyana dalilin kama wadanda abin ya shafa da kuma irin yanayin da aka tsare su a ciki.

Amnesty ƙara da cewa wadanda lamarin ya shafa da iyalansu kuma ya kamata a ba su damar neman hakkinsu ta hanyar doka da kuma samun diyya ko wasu hanyoyin da suka dace.

Ta ce akwai bukatar Hukumomi su tabbatar da an yi adalci ga wadanda suka rasa rayukansu a wannan mummunan lamari da ake ganin da an iya kauce masa.

Amnesty na wannan kira ne a daidai lokacin da Gwamnatin Nijeriya ta dakatar da kwamandan Jami’an na NSCDC kan abin da ya faru a Neja

Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya ba da umarnin dakatar da kwamandan hukumar tsaron ta Civil Defence na jihar Neja, Suberu Siyaka Aniviye, cikin gaggawa, biyo bayan zargin mutuwar matasan da ake zargi da haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba.

Lamarin mutuwar matasan dai ya haifar da barkewar tarzoma da zanga-zanga a wasu sassan birnin jihar, yanayin da ya sa Gwamnan jihar ta Neja, Umaru Bago, ya sanya dokar hana fita ta tsawon sa’o’i 24 a Minna.

Gidan talabijin na Channels ya ruwaito cewa dokar hana fita za ta fara aiki bayan an kammala sallar Juma’a, kuma za ta ci gaba da aiki har sai gwamnatin jihar ta bayar da wata sabuwar sanarwa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata