DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Wednesday, September 30, 2026
HomeLabaraiAmnesty International ta yi Allah wadai da kama matasan da suka sanya...

Amnesty International ta yi Allah wadai da kama matasan da suka sanya rigar Tinubu must Go’ a Maiduguri

Kungiyar Amnesty International ta yi Allah-wadai da tsare wasu mutane biyar da Rundunar ’Yan Sandan Jihar Borno ta yi a Maiduguri, bisa zargin sanya rigunan da ke dauke da rubutun “Tinubu Must Go”.

Mutanen da aka tsare su ne Baba Aji Gremami, Mustapha Abba Yemen, Abacha Mohammed Ali, Adam Umar Gubio da Abdulhamid Mohammed.

Amnesty ta ce tsare su da gaggawa da kuma gurfanar da su a gaban kotu kan zargin cewa suna da “niyyar haifar da barazana ga zaman lafiyar al’umma a yankin West End Roundabout da ke Maiduguri”, saboda sanya rigar da ke dauke da sakon adawa da gwamnati, ba laifi ba ne.

Kungiyar ta ce bayyana ra’ayin siyasa na daga cikin hakkokin dan Adam, inda ta bukaci hukumomi su gaggauta sakin mutanen tare da janye duk wani shiri na gurfanar da su bisa zarge-zargen da ta bayyana a matsayin marasa tushe.

Amnesty ta ce ’yancin bayyana ra’ayin siyasa ba mallakin wata jam’iyyar siyasa daya ba ne, tana mai zargin cewa gwamnatin Jihar Borno da ’yan sanda na kara kama da tsare ’yan jam’iyyun adawa da magoya bayansu.

Amnesty ta kuma ce hukumomin jihar sun koma amfani da dokoki wajen mayar da bayyana ra’ayin adawa laifi da kuma dakile muryoyin masu adawa da gwamnati.

Ta bukaci gwamnatin Gwamna Babagana Umara Zulum da kada ta matsa wa masu bayyana ra’ayin adawa cikin lumana, tana mai kira gare ta da ta kare ’yancin kowa na fadin albarkacin baki da yin tarayya, tare da mutunta doka.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata