DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, July 7, 2026
HomeKetareAmurka da Iran sun cimma yarjejeniyar dakatar da Yaƙi

Amurka da Iran sun cimma yarjejeniyar dakatar da Yaƙi

Amurka da Iran sun sanar da cimma yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙin da ya addabi Gabas ta Tsakiya tare da sake buɗe mashigar ruwa ta Hormuz, wadda ke da matuƙar muhimmanci wajen jigilar man fetur na duniya.

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa an kammala yarjejeniyar, inda ya ce jiragen ruwa za su iya komawa zirga-zirga cikin ‘yanci a mashigar Hormuz bayan watanni na rikici da takunkumi.

Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Iran, Kazem Gharibabadi, ya ce yarjejeniyar za ta kawo ƙarshen yaƙin nan take, tare da fara sabbin tattaunawa cikin watanni biyu domin cimma cikakkiyar yarjejeniyar zaman lafiya.

Rahotanni sun nuna cewa za a sanya hannu kan yarjejeniyar a ƙasar Switzerland a ranar Juma’a, yayin da Pakistan ta taka muhimmiyar rawa wajen shiga tsakani.

Sai dai har yanzu cikakkun sharuddan yarjejeniyar ba su fito fili ba. Kamfanin dillancin labarai na Iran, Mehr, ya ruwaito cewa Amurka za ta saki dala biliyan 12 daga cikin kadarorin Iran da aka daskarar kafin fara sabbin tattaunawa, tare da yiwuwar sakin wasu dala biliyan 24 a cikin kwanaki 60 masu zuwa.

A nata bangaren, gwamnatin Isra’ila ta ce dakarunta za su ci gaba da kasancewa a yankunan Lebanon, Syria da Gaza domin kare tsaronta, duk da sanarwar yarjejeniyar.

Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya, Antonio Guterres, ya yaba da matakin, yana mai cewa wata muhimmiyar dama ce ta kawo ƙarshen rikicin da ya jawo asarar rayuka da matsalar tattalin arziki a yankin.

Kasashen Saudiyya, Egypt, Burtaniya, Faransa, Jamus da Italiya sun yi maraba da yarjejeniyar, tare da nuna shirin rage wasu takunkuman da aka kakaba wa Iran idan aka samu dorewar zaman lafiya.

Sanarwar ta kuma haifar da saukar farashin man fetur a kasuwannin duniya, yayin da masana ke hasashen cewa sake buɗe mashigar Hormuz zai taimaka wajen daidaita harkokin makamashi da kasuwanci a duniya.

Mashigar Hormuz dai, na ɗaya daga cikin hanyoyin ruwa mafi muhimmanci a duniya, inda kaso mai yawa na man fetur da ake fitarwa daga Gabas ta Tsakiya ke bi ta cikinta. Yayin da buɗe ta ka iya rage matsin tattalin arziki da hauhawar farashin makamashi a ƙasashe da dama.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata