Jam’iyyar ADC ta sanar da tsohon Gwamnan Jihar Rivers kuma tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, a matsayin wanda zai yi wa Atiku takarar mataimakin shugaban ƙasa a zaben shugaban ƙasa na shekarar 2027.
A wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labarai na ƙasa na jam’iyyar, Bolaji Abdullahi, ya fitar a ranar Litinin, ya bayyana tikitin Atiku da Amaechi a matsayin “tikitin haɗin kai da ceto,” yana mai cewa haɗuwar jagororin biyu za ta taimaka wajen fitar da Najeriya daga matsalolin da take fuskanta.
Jam’iyyar ta ce zaɓen Amaechi ya biyo bayan shawarwari masu zurfi da kuma matsayinsa na wanda ya zo na biyu a zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa na ADC. Ta kuma yabawa gogewarsa a fannoni daban-daban na gwamnati, inda ya taba zama Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Rivers, Gwamna na wa’adi biyu, da kuma Ministan Sufuri.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito ADC ta ƙara da cewa haɗakar Atiku da Amaechi ya samar da tikitin da ke wakiltar yankuna daban-daban na ƙasar, tare da haɗa gogewa a shugabanci, tattalin arziki da gudanar da mulki.
Jam’iyyar ta bayyana kwarin gwiwar cewa wannan haɗin gwiwa zai ƙara ƙarfafa kawancen da take ginawa tare da jawo goyon bayan ‘yan Najeriya gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
Sai dai har yanzu babu wata sanarwa da Hukumar Zaben Nijeriya ta fitar kan fara karɓar takardun takarar zaɓen 2027, yayin da shirye-shiryen siyasa ke ci gaba da ɗaukar hankali a faɗin ƙasar.
