Tsohon gwamnan jihar Edo kuma sanatan da ke wakiltar Edo ta Arewa, Adams Oshiomhole, ya ce dan takarar shugaban Nijeriya na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ba shi da karfin siyasar da zai iya kayar da shugaba Tinubu a zaben 2027.
A cewarsa, Obi ba shi da cikakkiyar kima da tasirin siyasa, yana mai zargin sa da gazawa wajen tafiyar da rikice-rikicen cikin jam’iyyarsa da kuma warware su.
Oshiomhole ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi yayin wata hira da ya yi a shirin Mic On Podcast, inda ya kuma jefa ayar tambaya kan yanayin siyasar Obi da kuma sahihancin jagorancinsa.
