Gwamnatin Amurka ta bayar da jimillar tallafin kuɗi da ya kai dala biliyan 1.3 ga Nijeriya a cikin shekaru biyu, a wani bangare na tallafin da take bai wa ƙasashen waje.
Jaridar Punch ta rawaito Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ce ta wallafa haka a shafinta na sada zumunta, bayanin ya nuna cewa Nijeriya ta karɓi dala miliyan 879,102,695 a shekarar 2024, yayin da ta samu dala miliyan 646,404,163 a shekarar 2025, lamarin da ya sa ta zama ta biyar cikin ƙasashen yankin Sahara da ke karɓar tallafin Amurka.
A shekarar 2024, mafi yawan kuɗin tallafin ya fito ne ta hannun USAID, wadda ta bayar da dala miliyan 738,747,234 daga cikin jimillar kuɗin.
Sauran manyan hukumomin da suka bayar da gudunmawa sun haɗa da Ma’aikatar lafiya da jin daɗin jama’a ta Amurka da dala miliyan 112,061,903, sai kuma Ma’aikatar Harkokin Waje da ta bayar da dala miliyan 19,910,940.
Haka kuma, wasu hukumomi sun bayar da tallafi, ciki har da Hukumar gidauniyar ci gaban Afirka da ta bayar da kusan dala miliyan 2.4.
A shekarar 2025 kuwa, USAID ta sake bayar da mafi yawan tallafin da ya kai dala miliyan 597,602,944, yayin da Ma’aikatar lafiya ta bayar da dala miliyan 33,284,125, sannan Ma’aikatar Harkokin Waje ta bayar da dala miliyan 12,145,286.
Rahoton ya kuma nuna cewa wasu hukumomi sun bayar da kuɗaɗe a shekarar 2025, yayin da wasu da dama ba su bayar da komai ba, kamar yadda ya faru a shekarar da ta gabata.
Wannan bayani na zuwa ne a daidai lokacin da ’yan majalisar dokokin Amurka ke duba yiwuwar sanya ƙarin tsauraran sharudda kan yadda za a riƙa bai wa Nijeriya tallafi a nan gaba.
An bayyana cewa sabon kudirin kasafin kuɗi na shekarar 2027 na iya sa a riƙe har zuwa kashi 50 cikin 100 na tallafin, sai dai idan gwamnatin Nijeriya ta nuna ƙwazo wajen magance matsalolin tsaro, kare marasa ƙarfi, da kuma hukunta masu aikata laifuka.
