DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Wednesday, May 13, 2026
HomeSiyasaKungiyar ALGON ta goyi bayan tazarcen Tinubu a 2027

Kungiyar ALGON ta goyi bayan tazarcen Tinubu a 2027

Kungiyar shugabannin kananan hukumomi ta Nijeriya ALGON ta bayyana goyon bayanta ga Shugaban Bola Ahmed Tinubu, domin sake tsayawa takarar neman wa’adin mulki na biyu gabanin zaɓen shekarar 2027.

Jaridar Punch ta rawaito cewa an cimma wannan matsaya ne a yayin taron Majalisar zartarwar kungiyar karo na 54 da ya gudana a birnin Abuja.

Taron wanda Shugaban ALGON na ƙasa, Bello Lawal, ya jagoranta, ya samu halartar wakilai daga jihohi 36 da Abuja, tare da tsofaffin shugabannin ƙungiyar.

Shawarar marawa Shugaba Tinubu baya ta samu amincewa ne bayan wani tsohon shugaban ALGON, Alabi Kolade David, ya gabatar da ita, yayin da shugaban ALGON na jihar Filato, Anani Hamisu Mohammed, ya mara masa baya.

A cikin sanarwar bayan taron da aka fitar a ranar Lahadi, Mohammed ya ce ci gaba da mulkin Tinubu zai taimaka wajen ƙarfafa shugabanci a matakin ƙananan hukumomi tare da bunƙasa ayyukan gwamnati a matakin ƙasa.

Kungiyar ta bayyana cewa ta yanke wannan shawara ne bisa amincewa da tsarin gwamnatin Tinubu na “Renewed Hope Agenda,” wanda ta ce ya inganta ƙarfin tattalin arziki da ƴancin cin gashin kan ƙananan hukumomi.

A wani ɓangare na taron, ALGON ta sanar da dakatar da shugabannin ƙananan hukumomi uku bisa zargin aikata ba daidai ba.

Waɗanda aka dakatar sun haɗa da Zakari Iliyasu na ƙaramar hukumar Agwara a jihar Neja, Abubakar Danladi Abdullahi na ƙaramar hukumar Kaiama a jihar Kwara, da kuma Abba Shehu Tambuwal na ƙaramar hukumar Tambuwal a jihar Sakkwato.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata