DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, September 15, 2026
HomeKetareAmurka za ta bai wa Colombia tallafin tsaro na dala biliyan $1

Amurka za ta bai wa Colombia tallafin tsaro na dala biliyan $1

Gwamnatin Amurka ta sanar da shirin samar da tallafin tsaro na dala biliyan ɗaya ga sabuwar gwamnatin Colombia, ƙarƙashin sabon Shugaban ƙasar, Abelardo de la Espriella.

Jaridar Punch ta ruwaito ma’aikatar harkokin wajen Amurka ce ta bayyana hakan a ranar Juma’a, yayin da sabon shugaban ya karɓi ragamar mulkin ƙasar.

A cewar sanarwar, gwamnatin Shugaba Donald Trump za ta yi aiki tare da majalisar dokokin Amurka domin amincewa da kunshin tallafin, wanda aka tsara domin ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro tsakanin Washington da Bogotá.

Ma’aikatar harkokin wajen Amurkan ta ce tallafin na daga cikin sabon tsarin haɗin gwiwa da ƙasashen biyu suka ƙulla, wanda ake sa ran zai taimaka wa gwamnatin De la Espriella wajen cimma manufofin da suka shafi tsaro da sauran muradun ƙasashen biyu.

Sanarwar ta zo ne jim kaɗan bayan sabon shugaban Colombia ya hau karagar mulki, bayan ya yi nasara a zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar a watan Yunin 2026.

De la Espriella, ɗan siyasa mai ra’ayin irin na Trump, da ya doke abokin hamayyarsa, Iván Cepeda, da tazarar ƙuri’u ƙalilan.

Tun kafin zaɓen, Shugaban Amurka Donald Trump ya nuna goyon bayansa ga De la Espriella, lamarin da ya ƙara nuna kusancin manufofin shugabannin biyu musamman kan yaƙi da safarar miyagun ƙwayoyi da kuma matsalolin tsaro a yankin.

Sabuwar gwamnatin Colombia ta kuma bayyana aniyar ƙara haɗin gwiwa da Amurka kan harkokin tsaro, musamman wajen yaƙi da ƙungiyoyin masu aikata laifuka da kuma matsalar safarar miyagun ƙwayoyi.

Tallafin na dala biliyan ɗaya, wanda har yanzu yake buƙatar amincewar majalisar dokokin Amurka, na nuna ƙarin muhimmancin da gwamnatin Trump ke bai wa Colombia a manufofinta na tsaro a Latin Amurka.

Haka kuma, ana sa ran sabuwar haɗin gwiwar za ta ƙara danƙon dangantakar Amurka da Colombia a shekaru masu zuwa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata