Hunter Biden, ɗan tsohon shugaban Amurka Joe Biden, ya bayyana cewa ciwon dajin da mahaifinsa ke fama da shi ya bazu zuwa ƙasusuwansa, yana mai cewa rashin lafiyar na ƙara zama mai tsanani da radadi.
Hunter ya bayyana hakan ne a wata hira da BBC, inda ya ce ciwon ya bazu zuwa ƙasusuwan mahaifinsa da wasu sassan jikinsa. Ya bayyana yanayin a matsayin mai matuƙar wahala ga iyalansu, yana mai cewa ciwon dajin na jawo wa mahaifinsa tsananin ciwo.
A watan Mayun shekarar 2025, ne Joe Biden ya sanar cewa watanni huɗu bayan barin Fadar White House, an gano yana fama da wani nau’in ciwon dajin mafitsara mai tsanani.
Sai dai Biden ya bayyana a baya cewa yana samun kulawar likitoci kuma maganin da yake karɓa na tafiya yadda ya kamata. Ya kuma gode wa waɗanda ke nuna masa goyon baya da addu’o’i a yanayin da yake ciki.
Biden, wanda ya kasance shugaban Amurka daga 2021 zuwa 2025, ya fice daga takarar shugabancin ƙasar a watan Yulin 2024.
Inda rahoton jaridar Punch ya ce mataimakiyar shugaban ƙasa a wancan lokacin, Kamala Harris, ta maye gurbinsa a matsayin ‘yar takarar jam’iyyar Democrat, kafin ta sha kaye a hannun Donald Trump.
A cewar rahoton, Biden ya yana ƙara samun lokaci tare da iyalinsa yayin da yake ci gaba da karɓar magani kan nau’in cutar da ke damunsa.
