DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Sunday, April 19, 2026
HomeLabaraiAn gano wata masana'ntar da ake hada-hadar cinikayyar jarirai a Lagos

An gano wata masana’ntar da ake hada-hadar cinikayyar jarirai a Lagos

 

Jami’an rundunar tsaro ta Civil Defence a Nijeriya reshen jihar Lagos sun bankaɗo wani gida da ake zargin ana gudanar da harkar sayar da jarirai a yankin Okuju, Ilado, Badagry, inda suka ceto mata masu juna biyu 18 da yara 10 tare da cafke mutane biyu da ake zargi da tafiyar da wurin.

Rahoton jaridar PUNCH ya ce an gudanar da samamen ne daga daren Laraba zuwa wayewar garin Alhamis, inda aka kama Joy Okeke da Raphael Agwu.

Rahotanni sun ce yawancin matan sun samu shiga cibiyar ne ta hanyar wata talla da aka wallafa a dandalin Facebook.

Kwamandan rundunar ta NSCDC a Lagos Adedotun Keshinro ya ce sun samu sahihan bayanan sirri ne tsawon makonni uku kafin su kai samame gidan.

Ya ce ana yaudarar mata masu ciki da alkawarin kuɗi, sannan idan sun haihu ana karɓe jariran a sayar wa masu bukata.

Ya ƙara da cewa daya daga cikin matan da aka ceto ta yi ɓarin ciki, yayin da sauran 17 ke dauke da juna biyu.

Kwamandan ya ce lamarin babban laifi ne kan bil’adama, ya kuma bada tabbacin za a miƙa waɗanda ake zargi ga ’yan sanda domin gurfanar da su a kotu, yayin da za a miƙa matan da aka ceto ga hukumar yaki da masu safarar mutane ta NAPTIP domin kula da su.

Wasu daga cikin matan da aka ceto sun shaida cewa sun amince su mika jariransu bayan haihuwa domin a biya su kuɗi.

Wata ta ce an yi mata alkawarin naira miliyan 1, yayin da wata kuma ta ce an yi mata alkawarin naira miliyan 1.8.

Sun kuma ce ana ba su abinci kullum tare da kula da lafiyarsu, amma ba a barinsu su fita yadda suka ga dama.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata