An samu ƙarancin fitowar masu kaɗa ƙuri’a a wasu rumfunan zaɓe da ke garin Zuru yayin gudanar da zaɓen cike gurbin kujerar majalisar dokokin jihar Kebbi, inda jami’an hukumar zaɓen Nijeriya INEC suka kasance suna jiran masu zaɓe su iso domin kaɗa ƙuri’unsu.
Gidan talabijin na Channels ya ruwaito cewa a rumfar zaɓe ta Alhaji Budo da ke unguwar Rafin Zuru, jami’an INEC sun a shirya kayan aiki amma babu masu zaɓe a wurin domin gudanar da aikin zaɓen cikin sauri.
A wasu rumfunan da aka ziyarta a garin Zuru, an lura da ƙarancin layukan masu zaɓe yayin da mazauna yankin ke ci gaba da harkokinsu na yau da kullum, shaguna, gidajen mai da sauran wuraren kasuwanci sun kasance a buɗe kamar yadda aka saba.
A rumfar Mango Waje da ke yankin Manga a Zuru, an fara kaɗa ƙuri’a da misalin ƙarfe 9:14 na safe, inda aka samu kaɗan daga cikin masu zaɓe a layi.
Haka kuma zuwa ƙarfe 9:31 na safe, wasu jami’an INEC ba su karasa rumfunan da aka tura su ba, yayin da wasu kuma ke jiran umarni kafin su tafi wuraren aikinsu.
Shugaban jam’iyyar APC na jihar Kebbi, Abubakar Kana Zuru, wanda ya yi magana bayan ya kaɗa ƙuri’arsa, ya danganta jinkirin fitowar masu zaɓe da safiya da kuma ruwan sama da aka yi, yana mai bayyana kwarin gwiwarsa cewa jam’iyyarsa za ta yi nasara a zaɓen.
Ya ce duk da ƙarancin fitowar jama’a a lokacin fara zaɓen, tsarin ya gudana cikin kwanciyar hankali kuma akwai alamun cewa mutane za su ci gaba da fitowa yayin da lokaci ke tafiya.
Dan takarar APC na kujerar Sanatan Kebbi ta Kudu, Muhammad Jafar Gajere, shi ma ya kaɗa ƙuri’arsa a rumfar Alhaji Budo, inda ya yaba wa masu zaɓen da suka fito domin cika hakkinsu na dimokuraɗiyya.
A nasa ɓangaren, Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi, Salihu Dangoje, ya bayyana gamsuwarsa da yadda mata suka fito kaɗa ƙuri’a a rumfar Suffi da ke garin Zuru.
Jami’an tsaro sun kasance a dukkan rumfunan zaɓen da aka ziyarta domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro yayin gudanar da zaɓen kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito.
