DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, September 15, 2026
HomeLabaraiAn yi amfani da takardar bogi daga fadar shugaban kasa wajen kafa...

An yi amfani da takardar bogi daga fadar shugaban kasa wajen kafa hukuma PFIPC – Akanta Janar

Akanta Janar na tarayyar Nijeriya, Dakta Shamseldeen Ogunjimi, ya bayyana cewa an yi amfani da wata takardar bogi da aka danganta da fadar shugaban kasa wajen neman amincewar gwamnati domin kafa hukumar bogi mai suna Presidential Foreign Investment Promotion Council (PFIPC).

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Ogunjimi ya bayyana hakan ne a gaban kwamitin wucin gadi na Majalisar Wakilai da ke binciken yadda aka kafa da kuma yadda hukumar ta gudanar da ayyukanta.

Ya ce ofishinsa ya karɓi wata wasiƙa a watan Nuwamban 2024 mai ɗauke da lambar fadar shugaban kasa, wadda ta nemi a ƙirƙiri lambar gudanarwa (Administrative Code) ga hukumar domin gudanar da harkokin kasafi da kuɗi.

Ogunjimi ya ce bisa tsarin aiki, ofishinsa ya amince da buƙatar tare da ƙirƙiro lambar gudanarwar, kafin daga baya bincike ya tabbatar da cewa wasiƙar ba daga fadar shugaban kasa ta fito ba.

Ya kuma bayyana cewa bayan hakan, hukumar ta nemi a ba ta damar buɗe asusun gwamnati, da kuɗinta da kanta, da kuma a tura mata ma’aikata, sai dai ya jaddada cewa ba a taɓa fitar da ko sisin kwabo daga baitul malin gwamnati zuwa asusun hukumar ba.

A cewarsa, hukumar ta kuma nemi tallafin kafa ofis na Naira biliyan 27.4, amma gwamnatin tarayya ta yi watsi da buƙatar saboda babu tanadin kuɗin a cikin kasafin kuɗi.

Akanta Janar ya ƙara da cewa ko da yake Babban Bankin Nijeriya CBN, ya buɗe wa hukumar wasu asusun kuɗaɗen ƙasashen waje guda biyu, ba su fara aiki ba saboda hukumar ta kasa cika sharuddan da ake buƙata.

Kwamitin Majalisar ya bayyana cewa ya gano sama da takardu 29 da ake zargin an ƙirƙira domin yaudarar hukumomin gwamnati, yayin da rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da cewa an gurfanar da wanda ake zargi da jagorantar hukumar, Adeyemi Adeniyi, a gaban kotu bisa zargin damfara da ƙirƙirar takardun bogi.

Majalisar Wakilai ta kuma umarci Sufeto Janar na ‘yan sanda da ya gabatar da Adeyemi Adeniyi a gabanta nan da ranar Laraba domin amsa tambayoyi kan zarge-zargen da ake masa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata