DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Monday, September 14, 2026
HomeLabaraiTsohuwar shugabar hukumar NSIPA ta musanta karkatar da Naira biliyan 44

Tsohuwar shugabar hukumar NSIPA ta musanta karkatar da Naira biliyan 44

Tsohuwar shugabar hukumar NSIPA, Halima Shehu, ta musanta zargin karkatar da Naira biliyan 44, tana mai cewa babu wani kudi da aka taba gano an tura zuwa asusunta ko na wani daga cikin iyalanta.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Halima Shehu ta bayyana hakan ne a yayin wata hira da ta yi da gidan talabijin na Arise TV, inda ta ce tun kafin dakatar da ita daga mukaminta a watan Disamban 2023 ta kai rahoton wasu zarge-zargen almundahanar kudade ga hukumar EFCC da ICPC.

Ta ce bayan karbar ragamar hukumar, ta gano akwai raunin tsarin kula da harkokin kudi, lamarin da ta ce ta sanar da tsohuwar Ministar harkokin jin kai, Betta Edu, da sauran jami’an gwamnati.

A cewarta, an rika fitar da wasu kudade ba tare da amincewarta ko sa hannunta ba, inda ta zargi wasu masu kula da shirye-shiryen da aka nada da yin aiki ba bisa tsarin hukumar ba.

Halima Shehu ta ce maimakon a kare ta saboda fallasa abin da ta gano, sai aka dakatar da ita daga mukaminta bayan kusan makonni 10 da gabatar da korafinta.

Ta jaddada cewa binciken da EFCC ta gudanar bai gano ko sisin kwabo a asusunta, na iyalanta ko na abokanta ba.

A cewarta, kudaden da ake magana a kansu an tura su ne ga hukumomin biyan kudi da aka amince da su domin isar da tallafi ga wadanda suka cancanta a karkashin shirye-shiryen gwamnati.

Halima Shehu ta kuma bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya tabbatar an bayyana sakamakon binciken da ake gudanarwa kan harkokin hukumar NSIPA.

Ta ce mutuncinta shi ne babban abin da take alfahari da shi, tana mai cewa ko da ta yi wasu kura-kuran gudanarwa, ba ta taba satar kudaden da aka ware domin tallafa wa talakawa da marasa galihu ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata