‘Yan sanda a yankin Peel na lardin Ontario a kasar Canada sun kama wani tsohon kyaftin din jirgin saman Air Canada mai suna Geoffrey Wall bisa zargin yin amfani da takardun lasisin tuki na bogi.
‘Yan sanda sun ce bayan binciken watanni hudu, an gurfanar da Wall mai shekaru 59 da laifukan damfara da sauran tuhume-tuhume masu alaka da harkar jiragen sama.
A cewar hukumomin tsaro, Wall ya tuka sama da jirage 900 na cikin gida da na kasa da kasa tsakanin shekarun 2009 zuwa 2025 ta hanyar amfani da lasisin da ake zargin na bogi ne.
Binciken ya nuna cewa ko da yake yana da ingantaccen lasisin tukin jirgin kasuwanci, amma ba shi da lasisin Airline Transport Pilot Licence (ATPL), wanda shi ne mafi girman matakin lasisin da ake bukata domin mutum ya zama kyaftin din jirgi.
Hukumomi na ci gaba da bincike kan lamarin domin gano yadda aka samu wannan gibi na tsawon lokaci ba tare da an gano shi ba.
