Jam’iyyar NDC ta bayyana cewa tana ci gaba da kokarin sasanta rikicin da ya kunno kai tsakanin kungiyar Kwankwasiyya da wasu tsofaffin ‘yan jam’iyyar a jihar Kano.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran jam’iyyar na kasa na, Osa Director, ya fitar bayan wata ganawar sirri da aka gudanar tsakanin jagororin Kwankwasiyya, shugaban jam’iyyar na kasa, Sanata Henry Seriake Dickson, da shugabannin NDC.
Sanarwar ta ce an shirya taron ne domin lalubo hanyoyin warware sabanin da ke tsakanin bangarorin biyu tare da karfafa hadin kai a cikin jam’iyyar kafin babban zaben 2027.
A cewar jam’iyyar, Dickson da shugabannin NDC na ci gaba da tattaunawa domin tabbatar da cewa an bai wa dukkan mambobin jam’iyyar damar shiga harkokin tafiyar da ita ba tare da nuna bambanci ba.
NDC ta kuma jaddada cewa ba za ta tilasta wa kowa ne dan takara a Kano ko wata jiha ba, tana mai cewa jam’iyyar na ci gaba da mutunta tsarin dimokuradiyya da adalci wajen gudanar da zabukan cikin gida.
Jam’iyyar ta bukaci mambobinta da al’umma su yi watsi da duk wani sakamakon zaben fidda gwani da ake yadawa, tana mai bayyana cewa har yanzu ba ta fitar da suna ye daga kowace jiha ba.
Wannan rikici ya biyo bayan zarge-zargen da wasu shugabannin NDC na shiyyar Arewa maso Yamma suka yi wa jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, kan yunkurin mamaye tsarin jam’iyyar da kuma ware wasu masu ruwa da tsaki daga harkokinta.
Rahotanni sun nuna cewa shugabannin jam’iyyar a Kano da yankin Arewa maso Yamma sun kai koken lamarin ga hedikwatar jam’iyyar ta kasa domin neman daukin gaggawa.
Sai dai kungiyar Kwankwasiyya ta musanta rade-radin da ke cewa Kwankwaso na shirin ficewa daga NDC, tana mai cewa irin wadannan rahotanni ba su da tushe balle makama.
Jam’iyyar NDC ta ce tana fatan tattaunawar sulhun da ake yi za ta kawo karshen sabanin da ke akwai tare da tabbatar da hadin kai da kwanciyar hankali a jam’iyyar, musamman a Jihar Kano da ke da muhimmiyar rawa a siyasar Nijeriya.
