Gwamnonin jihohin Arewa maso Yamma sun kaddamar da wani sabon shiri domin rage talauci da bunkasa rayuwar al’ummar yankin, musamman mata, yara da sauran masu karamin karfi.
Sun bayyana hakan ne a wani taron tattaunawa da aka gudanar a Kano, wanda ya hada da, kwararru, kungiyoyin raya kasa da wakilan jihohin Arewa maso Yamma bakwai.
Taron ya mayar da hankali ne kan samar da hanyoyin rage talauci ta hanyar fadada shirye-shiryen tallafin jin kai, samar da damarmakin tattalin arziki da kuma nemo sabbin hanyoyin samun kudaden gudanar da ayyukan raya al’umma.
Da yake bude taron, Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa bai kamata a dauki tallafin da ake bayarwa a matsayin taimako kawai ba, illa a matsayin wata muhimmiyar hanya ta bunkasa jari ga mutane, karfafa zaman lafiya da habaka tattalin arziki.
Gwamnan, wanda mataimakinsa Murtala Sule-Garo ya wakilta, ya ce gwamnatin Kano ta dauki matakai da dama domin tabbatar da dorewar shirye-shiryen tallafin da take bayarwa na zamantakewa, ciki har da kafa dokar kare marasa galihu da kuma sabbin hukumomin kula da ayyukan jin kai.
Ya kara da cewa gwamnatin jihar na ci gaba da zuba jari a bangarorin ilimi, lafiya, koyar da sana’o’i, tallafa wa matasa da sauran shirye-shiryen da za su taimaka wajen inganta rayuwar al’umma.
A nata bangaren, Mataimakiyar Daraktan UNICEF a Nijeriya, Dakta Rownak Khan, ta ce har yanzu yankin Arewa maso Yamma na fuskantar manyan kalubale da suka hada da rashin abinci mai gina jiki, yawan mace-macen mata masu juna biyu da kuma karancin samun ayyukan lafiya da ilimi.
Ta jaddada cewa shirye-shiryen tallafin zamantakewa, musamman na bayar da tallafin kudi kai tsaye ga iyalai marasa karfi, na taka muhimmiyar rawa wajen inganta lafiyar yara, ilimi da walwalar al’umma.
Masu halartar taron sun nuna fatan cewa hadin kai tsakanin gwamnatocin yankin, kungiyoyin raya kasa da masu ruwa da tsaki zai taimaka wajen rage talauci, samar da ayyukan yi da kuma tabbatar da ci gaba mai dorewa ga al’ummar Arewa maso Yamma.
