DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, September 15, 2026
HomeSiyasaAPC ta lashe zaɓen cike gurbi na jihar Kano

APC ta lashe zaɓen cike gurbi na jihar Kano

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Nijeriya INEC ta ayyana ɗan takarar jam’iyyar APC, Rabiu Shuaibu, a matsayin wanda ya lashe zaɓen cike gurbi na mazabar tarayya ta Dawakin Kudu da Warawa da aka gudanar ranar Asabar a Jihar Kano.

Jami’in tattara sakamakon zaɓen, Farfesa Umar Sani, ne ya sanar da sakamakon zaɓen bayan kammala tattara kuri’un da aka kaɗa a faɗin mazabar kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

A cewarsa, Rabiu Shuaibu na APC ya samu ƙuri’u 35,356, wanda ya ba shi nasara a kan sauran ‘yan takarar da suka fafata a zaɓen.

Ɗan takarar jam’iyyar Allied Peoples Movement (APM), Lawal Garba-Haruna, ya zo na biyu bayan samun ƙuri’u 268 kacal.

Haka kuma, ɗan takarar jam’iyyar Labour Party (LP), Abubakar Yahaya-Muhammad, ya samu ƙuri’u 98 a sakamakon da INEC ta bayyana.

Da yake ayyana sakamakon, Farfesa Sani ya ce Rabiu Shuaibu ya cika dukkan sharuddan doka da ake buƙata domin lashe zaɓen.

Ya ƙara da cewa saboda haka an ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen kuma zababben wakilin mazabar Dawakin Kudu da Warawa a Majalisar Wakilai.

An gudanar da zaɓen cike gurbin ne domin maye gurbin marigayi Muhammad Danjuma-Hassan na jam’iyyar NNPP.

Marigayin ya rasu ne yayin da yake wakiltar mazabar a Majalisar Wakilai, lamarin da ya haifar da gurbin da doka ta tanadi a sake gudanar da zaɓe domin cikawa.

Sakamakon wannan nasara, jam’iyyar APC ta ƙara ƙarfafa matsayinta a Kano, yayin da sabon zababben ɗan majalisar zai wakilci al’ummar Dawakin Kudu da Warawa har zuwa ƙarshen wa’adin majalisar na yanzu.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata