Tsohuwar ministar albarkatun man fetur ta Nijeriya, Diezani Alison-Madueke, ta zargi hukumomin Birtaniya da ɓata mata suna da mutunci sakamakon shari’ar cin hanci da rashawa da aka shafe sama da shekara 13 ana gudanarwa kafin daga bisani kotu ta wanke ta daga dukkan tuhume-tuhumen da ake yi mata.
Alison-Madueke ta bayyana hakan ne a wata hira da ta yi da BBC bayan wata kotu da ke birnin London ta wanke ta daga zarge-zarge biyar da suka haɗa da karɓar cin hanci da haɗa baki wajen aikata cin hanci da rashawa, bayan dogon bincike da hukumar yaki da manyan laifuka ta Birtaniya (NCA) ta gudanar.
Tsohuwar ministar, wadda ta jagoranci ma’aikatar man fetur tsakanin shekarun 2010 zuwa 2015 tare da zama mace ta farko da ta shugabanci ƙungiyar OPEC, ta bayyana cewa binciken da shari’ar sun jefa ta cikin matsananciyar damuwa da tashin hankali na tsawon shekaru.
A cewarta, an hana ta yin tafiye-tafiye da kuma gudanar da ayyukanta na yau da kullum, lamarin da ya yi tasiri ga rayuwarta da martabarta, ta ce kuma farko ta san ba ta aikata laifukan da ake zarginta da su ba.
Alison-Madueke ta kuma yi zargin cewa wasu muhimman takardun da za su iya taimaka mata wajen kare kanta sun ɓace a Nijeriya bayan jami’an tsaro sun kai samame gidanta da ke Abuja a shekarar 2015, a cewarta daga cikin takardun akwai hujjojin biyan kuɗaɗen da aka kashe a madadinta.
Tsohuwar ministar ta ɗora alhakin abin da ya faru a kan hukumomin Nijeriya da na Birtaniya, tana mai cewa ya kamata hukumomin bincike da na shari’a su kasance masu taka-tsantsan musamman a shari’o’in da ke da alaƙa da siyasa.
Ta kuma yi ikirarin cewa watakila an mayar da hankali a kanta ne saboda matsayinta a masana’antar man fetur da kuma kasancewarta mace ta farko da ta kai irin wannan matsayi a Nijeriya da OPEC.
Sai dai martanin Hukumar NCA ya nuna cewa ta gudanar da cikakken bincike cikin adalci tare da haɗin gwiwar hukumomin ƙasashe daban-daban, kuma ta mutunta hukuncin alkalan kotun da suka wanke Alison-Madueke daga zarge-zargen.
Kazalika Alison-Madueke ta yi tambaya kan wasu kadarori da hukumomin Amurka da Nijeriya suka ce sun ƙwato suna da alaƙa da ita, tana mai cewa ba a ba ta damar kare kanta a kan waɗannan zarge-zargen ba, kuma tana fatan binciken abin da ya faru da waɗannan kadarori yanzu da ta samu ‘yanci.
