Ɗan takarar shugabancin Nijeriya na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya ce tsohon shugaban kasar, Olusegun Obasanjo, ba shi da ƙarfin zaɓen da zai iya samun nasara a zaɓe, yana mai cewa Arewa ce ta taimaka wajen kai shi ga zama shugaban ƙasa a 1999.
DCL Hausa ta ruwaito cewa Atiku ya bayyana hakan ne yayin ganawa da manema labarai a ranar Laraba, inda ya ce Obasanjo bai samu nasarar lashe jiharsa ko yankin Kudu maso Yamma ba a zaɓen shugaban ƙasa na 1999.
Atiku ya ce, “A shekarar 1999, bai ma iya lashe jiharsa ko Kudu maso Yamma ba, Arewa ce ta sanya shi ya zama shugaban ƙasa, ba shi da wata ƙima a zaɓe.”
Wannan kalami na zuwa ne a daidai lokacin da tsohon Shugaban ƙasar da tsohon mataimakinsa ke ci gaba da musayar kalamai kan tarihin dangantakarsu ta siyasa da kuma rawar da kowannensu ya taka wajen kafa gwamnatin da ta mulki Nijeriya daga 1999 zuwa 2007.
Takaddamar ta ƙara ɗaukar zafi ne bayan Obasanjo ya bayyana zaɓen Atiku a matsayin mataimakinsa a shekarar 1999 a matsayin “babban kuskuren” da ya aikata a lokacin shugabancinsa.
Tsohon shugaban ya kuma zargi Atiku da rashin biyayya da kuma hannu a wani yunkurin tsige shi daga kujerar shugaban ƙasa.
Sai dai Atiku ya yi watsi da wannan bayani, yana zargin Obasanjo da ƙoƙarin sauya tarihin abubuwan da suka faru da kuma amfani da abubuwan baya domin samun moriyar siyasa gabanin zaɓen 2027.
Atiku ya kuma kare rawar da ya taka a gwamnatin Obasanjo, inda ya ce ya taimaka wajen gina tsarin siyasar da ya ba su damar samun nasara a zaɓen 1999.
Da yake magana kan zaɓen 2027, Atiku ya jaddada cewa zai ci gaba da ba matasa damar shiga harkokin shugabanci idan aka zaɓe shi shugaban ƙasa.
Ya ce wasu daga cikin matasan da suka samu dama a lokacin da yake mataimakin shugaban ƙasa sun zama gwamnoni, ministoci, daraktoci da sauran manyan masu rike da mukaman gwamnati.
Atiku na neman kujerar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar ADC, bayan haɗa ƙarfi da wasu jiga-jigan ‘yan adawa domin tunkarar babban zaɓen 2027.
