Jam’iyyar PDP reshen jihar Gombe ta zargi gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya da nuna halin ko-in-kula game da rahotannin ɓulla da yaɗuwar cutar mashako ta diphtheria a sassan jihar.
A cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar PDP a jihar Gombe, Abdulkadir Ahmad Dukku, ya raba wa manema labarai a ranar Lahadi, jam’iyyar ta bayyana cewa rahotanni sun nuna ɓullar cutar a wasu jihohin shiyyar Arewa ta Tsakiya da Arewa maso Gabas, ciki har da jihar Gombe.
Sanarwar ta bayyana cewa cutar ta diphtheria tana da haɗarin gaske, inda kwayar cutar bakteriya ke kama maƙogwaro da hanyoyin numfashi. Alamominta sun haɗa da ciwon maƙogwaro yayin haɗiye abu, zazzaɓi da sanyi, kasala, fitar majina, da kuma tari mai ɗauke da jini a wasu lokutan, inda masu cutar ke fuskantar matsalar bugawar zuciya da shanyewar jijiyoyi.
Jam’iyyar ta ƙara da cewa, biyo bayan yaɗuwar cutar a yankin, an riga an rufe makarantu a jihohin Filato da Bauchi, yayin da ake gudanar da gangamin wayar da kan jama’a da bayar da riga-kafi a yankunan da abin ya shafa. Haka kuma, an sami rahotannin yaɗuwar cutar a maƙwabciyar jihar Yobe.
PDP ta nuna matuƙar damuwarta kan yadda rahotanni suka nuna cewa cutar, wacce ta fi shafar ƙananan yara, ta sa an kwantar da mutane tara a Asibitin Koyarwa na gwamnatin tarayya da ke Gombe, tare da samun wasu masu ɗauke da cutar a cibiyar kula da lafiya ta tarayya (FMC) da ke Kumo, da kuma manyan asibitocin Bajoga da Billiri.
Jam’iyyar ta ƙalubalanci Gwamna Inuwa Yahaya da ya nuna kyakkyawan shugabanci wajen inganta lafiyar al’umma maimakon karkata akalarsa kawai a kan gine-ginen hanyoyi. Ta buƙaci gwamnati ta fito fili ta yi wa jama’a bayani kan matsayin cutar a jihar, tare da gaggauta ɗaukar matakan kariya a makarantu da bayar da tallafin riga-kafi da magunguna kyauta domin daƙile yaɗuwarta.
A ƙarshe, PDP ta tunatar da gwamnatin APC mai ci cewa rayuwa da lafiyar al’ummar Gombe ba abin da za a riƙa yin riƙon sakainar kashi ba ne. Jam’iyyar ta ƙara da cewa jama’a suna da haƙƙin sanin nawa gwamnatin ta ware domin yakar cutar, musamman ganin yadda ake zargin gwamnatin da kashe miliyoyin nairori wajen ɗaukar mawaƙan Hausa daga Kano domin yi mata waƙa alhali rayukan al’umma na cikin haɗari.
