Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu, ya yi gargaɗi ga masu garkuwa da mutane, ‘yan bindiga da masu ɗaukar nauyin ayyukan ta’addanci su miƙa wuya ko kuma su fuskanci cikakken ƙarfin gwamnati.
A jawabin da ya gabatar ga ‘yan kasa domin bikin cika shekaru 27 na ci gaba da mulkin dimokuraɗiyya a Najeriya, Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta nuna jin ƙai ga duk wanda ke da hannu wajen hare-hare da sace-sacen jama’a ba.
Shugaban ya bayyana cewa sojoji da jami’an tsaro sun yi ajalin sama da ‘yan ta’adda 13,000 a bara kadai, tare da lalata cibiyoyin jagorancin ƙungiyar ta’addanci ta ISWAP a jihar Borno.
A cewarsa, yawan mutanen da ke mutuwa sakamakon hare-haren ta’addanci ya ragu da kashi 81 cikin ɗari idan aka kwatanta da shekarar 2015.
Tinubu ya kuma bayyana cewa sama da mayaƙa da iyalansu 124,000 sun ajiye makamansu tun daga shekarar 2023 ta hanyar shirin Operation Safe Corridor, wanda ke ba tsofaffin mayaƙa damar sake komawa cikin al’umma.
Shugaban ya ce gwamnatinsa ta ware Naira tiriliyan 5.41 domin harkokin tsaro a kasafin kuɗin shekarar 2026, mafi girma a tarihin ƙasar, domin yaƙi da ta’addanci da sauran matsalolin tsaro.
Ya kuma bayyana cewa an amince da ɗaukar sabbin ‘yan sanda sama da 50,000 tare da dubban sabbin sojoji domin ƙarfafa jami’an tsaro a faɗin ƙasar.
Sai dai ya ce bikin Dimokuraɗiyyar bana ya samu ɗan raguwar farin ciki saboda ci gaba da tsare ɗalibai da malamai da aka sace a jihohin Oyo da Borno, inda ya nuna fatan za a ceto su cikin koshin lafiya.
Dangane da matsalar wutar lantarki, Tinubu ya ce lokacin da ya karɓi mulki a 2023 ya tarar da ɓangaren wutar lantarki na fama da ƙarancin samar da wuta, matsalolin iskar gas da kuma tsofaffin kayayyakin rarraba wuta.
Ya ce gwamnatinsa ta aiwatar da dokar Electricity Act, wadda ta bai wa jihohi damar samarwa, watsawa da rarraba wutar lantarki, tare da shirin tara Naira tiriliyan 4 domin biyan tsoffin basussukan da ke damun ɓangaren.
A ɓangaren tattalin arziki kuwa, shugaban ya ce kuɗaɗen shiga na tarayya sun ƙaru, yayin da fitar da kayayyakin da ba man fetur ba zuwa ƙasashen waje ya ƙaru da kashi 21 cikin ɗari a shekarar da ta gabata.
Ya amince cewa har yanzu ‘yan Najeriya da dama na fuskantar matsin tattalin arziki, amma ya jaddada cewa gwamnatinsa na ci gaba da aiki domin rage hauhawar farashi, samar da ayyukan yi, ƙara samar da abinci da inganta rayuwar al’umma.
Tinubu ya yi kira ga ‘yan Najeriya su kasance masu haɗin kai wajen yaƙi da rashin tsaro, yana mai cewa aikata laifi ba ya ga ƙabila ko addini.
