Kocin Paris Saint-Germain, Luis Enrique, ya bayyana cewa babu wata ƙungiya da ta fi PSG ƙarfi a yanzu, yana mai nuna cikakken yarda da ƙarfinta da damar lashe gasar zakarun Turai.
Kamar yadda Fabrizio Romano ya wallafa a shafinsa na X, Enrique ya bayyana hakan ne bayan wasan da PSG ta buga da Bayern Munich ranar Laraba.
Kocin ya tuna da kalaman da ya yi tun a matakin rukuni na gasar, inda ya sake nanata cewa har yanzu yana da cikakken imani da ƙungiyarsa.
Ya ce, “Kun tuna abin da na faɗa a matakin rukuni? Babu ƙungiyar da ta fi mu. Ina sake maimaita hakan. Muna yarda da wannan ƙungiya.”
Luis Enrique ya ce ‘yan wasansa na da ƙwarewa da ƙarfin guiwar fafatawa da kowace ƙungiya a matakin ƙololuwa.
Rahotanni sun nuna cewa PSG za ta kara da Arsenal a wasan ƙarshe na gasar UEFA Champions League ta kakar 2025/2026, wanda za a buga ranar 30 ga Mayun 2026 a filin wasa na Puskás Aréna da ke Budapest, Hungary.
