Tsohon Gwamnan jihar Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso ya goyi bayan matakin da jam’iyyar NDC ta ɗauka na ware tikitin takarar shugaban Nijeriya na shekarar 2027 ga yankin Kudu, yana mai cewa hakan na nuna tsarin rabon iko na jam’iyyar da kuma ƙoƙarinta na tabbatar da adalci.
Kwankwaso ya bayyana hakan ne a yayin babban taron jam’iyyar na ƙasa da aka gudanar a Abuja, inda ya ke jawabi ga wakilai, magoya baya da sauran masu ruwa da tsaki a jam’iyyar, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Haka kuma ya buƙaci ’yan Nijeriya da magoya bayan jam’iyyar da su shiga cikin shirin wayar da kai da tattara magoya baya kafin zaɓen 2027.
Wannan goyon baya ya zo ne awanni kaɗan bayan da jam’iyyar NDC ta amince a hukumance da kudurin ware tikitin takarar shugaban ƙasa na 2027 ga yankin Kudancin Nijeriya na wa’adin shekara huɗu.
An amince da kudurin ne bayan wata shawara da ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Ogbaru a Jihar Anambra, Afam Victor Ogene, ya gabatar.
Da yake sanar da wannan mataki, shugaban jam’iyyar na ƙasa, Moses Cleopas, ya ce wannan tsari wani ɓangare ne na babbar dabarar rabon iko da nufin daidaita muradun yankuna a cikin haɗakar jam’iyyun adawa.
