Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, ya bayyana cewa dalibai da malamai da aka yi garkuwa da su a ƙaramar hukumar Oriire har yanzu suna hannun masu garkuwa a yankin tsohon Gandun Dajin Oyo.
Makinde ya ce duk da yake an yi kwanaki 27, tun bayan sace su daga makarantu a al’ummomin Yawota da Ahoro-Esinle, hukumomin tsaro na ci gaba da gudanar da bincike da ayyukan ceto domin tabbatar da an kuɓutar da su cikin koshin lafiya.
Gwamnan ya bayyana cewa bayanan sirri da hukumomi suka tattara sun nuna cewa waɗanda aka sace suna cikin tsohon yankin Gandun Dajin Old Oyo National Park, wanda ya mamaye kusan murabba’in kilomita 2,500 a sassan ƙananan hukumomi goma na jihar.
Ya ƙara da cewa girman dajin da wahalar yanayinsa na daga cikin manyan ƙalubalen da jami’an tsaro ke fuskanta yayin gudanar da aikin ceto, amma ya tabbatar da cewa ana bin duk wata sahihiyar masaniya domin ganin an ceto daliban da malamansu lafiya.
Makinde ya kuma yi kira ga mazauna jihar da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro haɗin kai tare da kai rahoton duk wani abu da suka gani mai tayar da hankali, yana mai gargadin jama’a da su guji yaɗa jita-jita da bayanan da ba a tabbatar da su ba saboda hakan na iya kawo cikas ga aikin ceto.
